FreeArewaPen original
BAKAR TAADA
- 1views
- 51chapters
- 0audios
- words
- 0likes
Share:
The story
Synopsis
No synopsis yet.
Sample · Page 1
1&2.*10-02-23.**1:00pm.**JAN KUNNE**KADA A TA'BA MINI LABARIN NAN, KO KARANTA SHI A KOWACCE IRIN KAFA TA SADARWA BA TARE DA IZININA A RUBUCE BA*.*IDAN KUMA AKA YI KARAMBANIN TABAWA, ZA'A FUSKANCI TUHUMA DAGA LAUYANA BAR MUSTAPHA ISA GWARAM*.*GARGADI*.*WANNAN LABARIN KIRKIRARREN LABARI NE**BA SHI DA ALAKA DA KO WANNE MAHALUKI*.*IDAN KIN CI KARO DA RAYUWAR DA TA YI KAMANCECENIYA DA TA KI, KO WANINKI, TO ARASHI NE*.*DOMIN MANUFAR MARUBUCI ISAR DA SAKO DA HANNUNKA MAI SANDA A CIKIN ZAMANTAKEWARMU*.*LITTAFAN SURAYYA BASA NUFIN HABAICI KO SHAGUBE GA RAYUWAR WANI KO WATA.**NA GODE*.*GODIYA GA**SADIK ABUBAKAR**NA GODE MADALLAH*.*GAISUWAR GIRMA GA IYAYENA KUMA MARUBUTA**HAJ SALIHA ABUBAKAR ABDULLAHI ZARIA*.*HAJ HAFSAT C SODANGI*.*HAJ MARYAM KABIR MASHI*.*YABO GA**K'AWATA JAMILA JANAFTY**IDAN DA WANDA NA GAMSU DA TULIN SOYAYYARTA GA RUBUTUNA DA CIGABANSA TO KE CE**DUK WATA KALMA TA YI KA'DAN TA FAYYACE GIRMAN SHA'ANINKI A WAJENA**INA FATAN UBANGIJI YA SHIGA AL'AMARIN KI, YA BAKI MIJI NA GARI*.*GAISUWAR SADA ZUMUNCI GA MARUBUTA**Sumayayyah Takori**Binta Umar Abbale*Fadilah lamido*.*Hassana D'anlarbawa**Zainab MAZAWAJE**Lubna Sufyan**Nazifa Nashe**Ayusha Muhd**Nana Diso*.*Kulsum Baffah*.*Safiyya Um Abdul**Umm Asghar*.*Aisha Dansabo**Aisha jos**Da dukkan Y'an kungiyarmu ta lafazi*.*FATAN ALHERI GA IYAYEN D'AKINA*.*HAJ HALIMA D'ALHA SHEHU**HAJ RABI SANI**HAJIYA HALIMATUS SA'ADIYA**HAJIYA HADIZA FARI*.*ALLAH YA HA'DA Y'AY'ENKU DA MUTANAN DA ZASU MUSU KARAMCI FIYE DA YADDA KUKE MINI, INA MATU'KAR GODE MUKU*.*TUKUICIN LABARIN SUKUTUM GA**AISHA MUHD LAME**ALLAH KA SO AISHA, KA FARANTA MATA, KA BIYA MATA BU'KATUN TA NA DUNIYA, KA BATA BABBAN RABO A LAHIRA*.*IDAN AKWAI WANDA JINI BAI HA'DAMU BA, NA KE DAKACEN INA MA JINI YA RATSA TSAKANINMU TO AISHA LAME CE MAI KAYAN Y'AN GAYU TA ORIFLAME**SURAYYA DEE TA GODE, TA YABA MIKI, UBANGIJI YA TAYA NI GODE MIKI*.*Doka mi lamba ta 68 ta nuna cewa satar fasaha Babban laifine da yake dai-dai da satar Dukiya**BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM*.*SHIMFI'DA*.Sunana Asiya Sani Toro.Amma mafi yawa da Yabi ake kira na a dalilin mahaifiyata ta yi aikin Hajj da ni a cikinta.Mama ce kawai bata kira na da hakan sai Asiya saboda tana adawa da Yabi tunda ana nufin nima Hajiya ce.Gidanmu babban gida ne a garin na Toro domin ko yaro k'arami ka tambayi gidan Marina zai nuna maka. A dalilin asalin kakanmu da ya zo daga Kano ya fara kafa wannan sana'ar a garin. Fiye da shekaru saba'in kenan, amma har yau ba'a juya wa sana'ar baya ba, duk da dai an zamanantar da ita, ba kuma cikin gidan ake yin ta ba saboda warinta.Gidanmu babban gida ne k'warai da gaske.Idan na ce babban gida ina nufin mai d'auke da ahali daban daban masu yawa.Ko a k'ofar mahaifinmu Alh Sani (Baban Marina) da shi ne babba mata uku ne.Hajiya Habiba ita ce uwargidan mahaifinmu, mace ma...
Contents
Table of contents
Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.