CANJIN MUHALLIFree

ArewaPen original

Teen fictionFreeOngoing

CANJIN MUHALLI

  • 1views
  • 3chapters
  • 0audios
  • words
  • 0likes
Start reading

Share:

The story

Synopsis

ongoing

No synopsis yet.

Sample · Two

  A airpot ɗin JFK New york jirginsu Jidda ya sauƙa da yamma bayan ya shafe awanni fiye da sha biyu yana tsala gudu a sararin samaniya. Tun da aka fara tafiyan zuciyar Jidda take tsinkewa ba tare da dalili ko tsoro ba, haka kurum sai ta fara wasiwasin wannan Canjin Muhallin da tayi, anya bata yi gaggawar yanke hukunci ba? Anya baza ta yi dana sanin hakan ba? Shin ya rayuwarta zata kasance a cikin mutanen da addininsu, ƙabilarsu da kuma kalar fatarsu take da banbanci? Wani irin tarɓa zata samu daga garesu bayan tana da tabbacin suna wulaƙanta baƙar fata? Kwakwalwarta cike da ire-iren wannan tunanin ta bi layi suka fito daga cikin jirgin, bayan wasu lokuta ta gama clearing immigration da duk wani bincike da za'a mata a matsayinta na baƙuwa a ƙasar, daga nan ta nufi hanyar da zai sadata da wajen airpot ɗin inda ta tabbatar yayarta Haajar ke jiranta cike da murnar ganinta.  Murmushi ne ya suɓuce a fuskarta dalilin ganin yayar tata cikin mutane irinta da suka zo tarɓan ƴan'uwansu. A tsakiya suka haɗu suka rungume juna ƙamƙam lokaci ɗaya kuma hawaye ya taru a idanunsu har yana bin ƙuncinsu."Hey, stop crying." Faɗin Haajar tana share hawayen fuskar Jidda."Ke ma ki daina." Jidda ta mayar mata da martani tana ƙoƙarin danne kukan da yake son kwacewa daga bakinta."Na daina. Sannunki da isowa ya hanya?" Faɗin Haajar bayan ta nitsu ta kuma share hawayen fuskarta."Alhamdulillah, sai dai ina jin yunwa don na kasa cin komai na cikin jirgin. Kuma haka kawai sai zuciyata take ta tsinkewa." Ta bata amsa a lokacin da suka fara tafiya zuwa waje inda motar Haajar take."Ya Salam. Hakan yana faruwa domin ina tuna ranar da zan dawo Newyork bayan aurena da Hamza I felt that. I even asked myself did I make the right decision? So with time zai wuce, dama when you make a big decision like that it's natural to be afraid of the outcomes. Ki kwantar da hankalinki da zarar kin fara zuwa makaranta zaki ji kamar a nan kika yi duk rayuwarki." "Speaking of which, ina mai jan kunne?" Jidda ta tsokani mijin Haajar tana murmusawa."Yana can gida yace ya bamu sarari mu yi bonding a kan hanya." Ta ƙarisa maganan tana dariya."Ko kuma ya barki da tafiya ba." Itama Jidda ta saka dariya a lokacin da suke fita mashigar airpot ɗin suka nufi parking space inda Drivern su Haajar mai suna Mr Lee yayi parking ɗin motarsu suka shiga baya suka zauna. A hanyarsu ta komawa gida suka tsaya a McDonald's Haajar ta sayo Burger da Coke ta bawa Jidda tana cewa,"Ki tare yunwar da wannan, domin akwai tafiya a gabanmu, and kar ki cika cikinki don na miki girki all your favorite's" Jidda da bakinta yake cike da abincin kaɗa kai kawai ta yi, sai da ta haɗiye sannan tace,"Ohhh no! Har na manta akwai sauran tafiya a gabanmu wallahi." Ta koma jikin seat ɗin ta kwanta a kasalance."...

Continue reading free chapter

App exclusive

Continue “CANJIN MUHALLI” in the app

The author limited this story to mobile. Open the app to read, listen, and keep your place.

Download on the App StoreGet it on Google Play