MANSOORFree

ArewaPen original

MANSOOR

  • 1views
  • 51chapters
  • 0audios
  • words
  • 0likes
Start reading

Share:

The story

Synopsis

ongoing

No synopsis yet.

About the author

Am not just to here to write but to entertain and touch the heart of the readers

More from @sadnaf

Sample · Chapter 2

*MANSOOR*     *NA SADNAF**ADABI WRITERS ASSOCIATION**PAGE 2*     Haka na tsaya sai da suka bacewa ganina na ja kafafuna da naji yamin sanyi kalau na zauna akan kujera na dora hannayena biyu a kai dan nasan dagaske na shiga uku wacce Allah ya jarrabceni da so matar Aure ce,yanzu daga Ina zan fara,ko da nake zaunen ji nake kamar na Kara komawa Ajinsu nayi ta kallon ta har yanzu gizo take min.Bansan tsawon lokacin da na dauka a zaune Ina tufka da warwara ba so nake naga ko zan iya danne zuciyata na hakura da ita tunda har tace min ita matar Aure ce,ba ta yarda za'ayi ta iya kulani tunda tana da Aure,amma bana Jin zuciyata ta shirya ciremin san ta a raina dan ji nake ma ganinta nan da nayi ya kara rura min wutan kaunarta.Kamar Wanda aka mitsina batare da tunanin komai ba na fita waje na samu waje na tsaya Ina kallon department din su,ni level 2 nake d'auka ita kuma tana level 1 da alama sabuwar daliba ce ma shi yasa ban tab'a ganin ta ba.Haka na zauna a wajen Ina tunanin yadda zan samu a Maidani Ajinsu na ringa ganinta kasan zuciyata kuwa so nake na hakura da abinda bazai yu ba,Humairan ma ba mai sakin fuska bace ballantana nace idan na dameta da magiya kila ta taimaka ta bani lambarta,duk da nasan Haramun ne kula matar wani,amma naki bari zuciyata ta gano haramcin.Ganin dalibai sun fara fitowa yasa na fara wurga ido naga ta inda zan hangota kirjina sai bugu yake,sai da daliban da yawa suka gama wucewa na hango ta ta fito ita da wanan yarinya da ta kwalla mata kira,ko barin da nake bata kala ba hirarsu kawai suke har suka wuceni,umarnin da zuciyata ta bani kawai nabi dan naga alamar bani da control gabadaya akan kaunar yarinyar,kulle office dina nayi da sauri na fito nayi wajen motata dan Ina iya ganosu sun kusa barin cikin makarantar,da sauri na ja motar na fita na tsaya nesa da makarantar Ina kallonsu ta mudubi so nake ko yayane na samu na shawo kanta ko iya lambar ce ma ta bani,dayar ce ta fara tsayar da abin hawa tayi tafiyarta Humairan na daga mata hannu kafin naga ta tsallaka ta fara tafiya bata wajen da motata take ba,ashe shiyasa bana ganin ta ta canza hanya ne.A nutse take tafiya Ina kallon ta ta glass a daidai lokacin da na koma ta hannun da take tafiya sai da na wuceta sosai nayi parking kanta a sunkuye sam bata ma lura dani ba.Ido kawai na kura mata kirjina na bugu, wallahi tunda nake ban tab'a Jin irin haka akan mace ba dan tafiyarta kawai ma fusgata take har ta kusa wuce motata bata dago ba,sai da na fito daga motar nace "Humaira"Cak ta tsaya ta juyo a hankali muka hada ido,fuskarta tayi saurin hadewa ta ja tsaki ta cigaba da tafiya ni kuwa da sauri na sha gabanta cikin kwantar da murya kamar nayi kuka Ina jina a cikin wani yanayi da naga na dan tsaya kusa da ita nace "Humaira dan Allah...

Continue reading free chapter

App exclusive

Continue “MANSOOR” in the app

The author limited this story to mobile. Open the app to read, listen, and keep your place.

Download on the App StoreGet it on Google Play