Rayuwar SajidaFree

ArewaPen original

RomanceFreeCompleted

Rayuwar Sajida

  • 1views
  • 4chapters
  • 0audios
  • words
  • 0likes
Start reading

Share:

The story

Synopsis

completed

No synopsis yet.

Sample · Rayuwar Sajida

*** TACI GIDA 💫💫      (Rayuwar Sajida)Story   and     WrittenByMum sayyid 💫💫💖THE TALENT TROUPE WRITER'S 💖Page 3_______Anan cikin garin katsina aka ajiye Rakiya Yusuf gidanta yayi kyau Masha Allah iyayenta sunyi kokari,amma saboda rashin tsoron Allah haka Sajida ta zauna ta dinga kushe gidan nan tun ana biye mata har aka gaji aka barta da halinta dan kowa ya gane hassada ce ke damunta ba komai ba Kuma ta kasa danne zuciyarta ta boye.Gida na sai yafi haka kyau da tsaruwa dan har yan aiki zan dauko ni bana son rainin wayo ai iyayena ma su shirya zabga mun kaya dan ba dan masu karamin karfi ke Sona ba,Inaga ma ba garin nan zan zauna ba.Haba Sajida kin damemu ki bari in lokacin yayi ma gani,yanzu ki barmu musha iska mana cewar wata kawarsu,ai kuwa kamar jira take Yi ta rufeta da bala'i ni wlh ki fita a idona don ni ba kanwar lasa bace in kina cin kasa ki kiyayi ta shuri zan miki dukan mutuwa anan babu mai tsaya miki.Fada ne ya kaure dakyar aka raba fadan saboda waccan ma gidan ta tarar yar bala'i ce sai da manya suka shiga kafin Sajida ta suri jakarta tayi hanyar fita,"tafiya zakiyi akan abinda bai Kai ya kawo ba shine zaki tafi ko ba dan kowa ba kyayi dan Rakiya.Jamila babu ruwanki ai itama Rakiyar tana Ji ana min rashin kunya bata ce komai ba dan haka kunga tafiyata wawaye kawai.Oh ni Jamila wanan kawartawa akwai bala'i zata Sha wahala a wajen miji da danginsa Kam in batayi hattara ba.Sha'anin gabansu suka cigaba dayi har aka gama kowa ya watse aka bar amarya da angonta.Sati daya zagayo akayi na Binta sulaiman itama ansha Biki sosai amarya tayi kyau sosai gashi mijinda ta aura mai hannu da shuni ne anyi bajinta sosai dan su kansu kawayen amarya ba karamin kudi suka samu a bikin ba.Ko da aka Kai amarya,gida ne na gani na fada kowa sai murna da son barka yake mata na samun wajen zama mai kyau sai fatan Allah yasa zaman yafi gidan kyau ya kauda fitina da masu hassada.Suna shiga cikin gidan Sajida ta kasa boye hassadar ta nan take fuskarta ta chanza ko zama ta kasa Yi sai kallon koina take tana tabe baki,daga karshe ma cewa Jamila tayi ciwon ciki na damunta zata koma gida,rakota tayi har bakin hanya ta hau adaidaita sahu ta nufi gida.Suna fara nisa ta fashe da kukan da ita kanta bata san kuka me takeyi ba,sai daga baya zuciyarta take gaya mata ai ke ya kamata ki samu wanan gidan ba Binta ba duk kyan nan nawa ace bansamu gida irin wanan ba sai ita,tsananta kukan tayi har suka Isa tana Kuka ga wani nauyi da takeji a kirginta.Gidansu ta fada tana cigaba da kuka Mami ce ta biyota hankali tashe ta dauka wani abun ne ya faru take wanan uban kukan.Lfy wani ne ya rasu ko fasa aure akayi ta tambaya duk a lokaci daya.A'a Mami duk ba daya.Toh ...

Continue reading free chapter

App exclusive

Continue “Rayuwar Sajida” in the app

The author limited this story to mobile. Open the app to read, listen, and keep your place.

Download on the App StoreGet it on Google Play