FreeThe story
Synopsis
No synopsis yet.
Sample · DOGON BURI
✨DOGON BURI ✨ *_(Not all glitter are gold)_* *_ Story_* *_And_* *_Written_* 🔽 *_Mum sayyid 💫💫 💫_**Dukkan godiya ya tabata ga Allah subahanahu wata'ala* *_Wanan shafin sadaukarwa ne ga dukkan masoyana da wanda na sani da wanda ban sani ba_*💖الحَمْدُ ِلله سبحان الله الله أكبر💖 ﷽ Bismillah........ ✍️💋*TITAN'S OF TALENT*💋*Marubuta masu aiki da fasahar zamani , zalar ilimantarwa,fadakarwa dakuma nishadantarwa***(T .O.T)***Breathe in courage, breathe outfear, together we stand***Alkalaminmu abin alfaharn mu*Page 2____Tana bude kofar gidan kawun ta ta gani tsaye fuskarshi a daure kamar bae taba sanin wani abun ba wai fara'a,kallonta yakeyi sama da kasa kamar ya rufeta da duka "Ke dan ubanki ina dankwalinki,zaki fito ki bude qofar gida ba suturar kirki balle dankwali anya Asma'u tana koya miki abun kirki kuwa,dan wanan hanyar ba mai bullewa bace a gareku" Wani irin kallo take mishi tunda ya fara magana har ya gama a lokacin da yake magana bae kula ba sai da ya karasa magana tukkuna ya kalli fuskarta yaga kallon da take masa na raini wayyo duka ya kawo mata ta goce ta fada cikin gida tana kurma ihu tare da zubewa a tsakar gida tana burburwa kamar wacce aka zubawa ruwan zafi sbd makirci,da gudu Ummi ta fito daga daki zaninta a hannu daga ita sai undies ta fito tsakar gida gun Aleena ta dire tana tambayarta "Waye ya miki wani abun daga zuwa bude qofa naji an kwankwasa qofa kin tafi budewa sai dae naji kina wanan ihu da burburwa na shiga uku ni Asma'u " Jijigata ta cigaba dayi tana hawaye itama ilahirin jikinta rawa yakeyi,dakyar ta daidaita nutsuwarta ta ce "Kawu Musa ne ya kwankwasa qofa Ina budewa ya wankeni da mari kafin nayi magana ya Kara min wani ya wurgoni cikin gida Jamar kayan wanki"cikin sheshekar Kuka take magana kirginta nata sama da kasa kamar numfashinta zai dauke."Mu me??? "Musa"ta Kara fada cikin ihun kuka."Yana Ina yau zai ga rashin mutunci mai wasali wlh"tashi tayi ta daura zaninta gam kamar me shirin ruwa dambe ko gudu,fuskarta ba annuri akanta Sam."Yana qofar gi....! Ko karasawa batayi ba ta nufi qofar gida jiki ta na rawa,tana Isa ko gaisawa basuyi ba ta ce "Yanzu Kai Musa! Abinda kayi mun da safiyar nan ka kyauta kenan,kai a rayuwar ka kafi so ka zo ka tada mun hankali shine kawai abinda kafiso yarinyar yanzu me tayi ...
Contents
Table of contents
Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.