FreeArewaPen original
Fatu A Birni
- 1views
- 7chapters
- 0audios
- words
- 0likes
Share:
The story
Synopsis
No synopsis yet.
Sample · 1 Tsautsayi
CIKIN TASHA: A cikin cinkoson mutanen dake fitowa daga cikin motar hayar har da wata matashiyar budurwa, wacce in ka lura da yadda take waige-waige tana zare idanu zaka tabbatar yau ne farkon shigowanta garin Gombe, wanda ake musu kirari da 'Gombawa d'iban fari, ba'a kwana daku ba an tashi daku'. Itama FATU haka ya kasance da ita domin yanzu misalin karfe bakwai ne na safe. Sanye take cikin atamfa koriya riga da zani, sai babban hijabi bak'i da ta sanya wanda ya kai har k'aurin kafarta. Duk da girman hijabinta bai hanata mannawa fuskarta nik'abi ba wanda hakan yasa ba'a ganin komai na jikinta sai k'afarta, tafin hannunta da kuma kwayar idanunta da suke farare kamar madara. Daga ganin yanayinta kadai zaka gane ita bak'uwa ce a cikin wannan gari mai tarin jama'a. Fatu matsawa tayi gefe ta tsaya inda babu mutane ta cigaba da dube dubenta tana neman hany...
App exclusive
Continue “Fatu A Birni” in the app
The author limited this story to mobile. Open the app to read, listen, and keep your place.