FreeArewaPen original
KWANTAN ƁAUNA
- 1views
- 102chapters
- 0audios
- words
- 0likes
Share:
The story
Synopsis
No synopsis yet.
About the author
Writing is my passion❤️😍
Sample · Trailer
*KWANTAN ƁAUNA* FitattuBiyar*ƊANƊANO* ****Dare yayi duhu ya mamaye gari hannunka baka gani saboda yadda garin yayi duhu matuk'a, yayi tsiitt baka jin motsin komai ko ba'a fad'a ba yanayin garin zai tabbatar maka da dare ya tsala. Mata ne guda biyu suke tafiya da sassarfa cikin siririyar hanya mai d'auke da ciyayi da shuke-shuke, sauri suke sosai babu kamar wacce take a gaba, ta bayan biye take da ita duk inda ta jefa k'afarta itama nan take saka tata.Hasken aci balbal suka hango a gaba hakan ya saka ta k'ara ƙaimi wajan sassarfa har suka iso inda suke gano hasken, ta kalli wacce take bayanta tace, "Dakata a nan." Cikin girmamawa tace, "An gama ranki ya dad'e, ki fito lafiya." Gaba tayi zuwa inda hasken yake da sauri kamar zata kifa domin burinta ta isa wajan, dutse ne babba a wajan sai yadi kalar ja da aka yane dutsen da shi da kawunan rago a sak'ale anyi ado da su, wasu suna zubar da jini wasu sun fara bushewa wasu kuma sun zama k'ashi.Zubewa tayi a k'asa tace,"Ta haihu! Ta haifi yara maza har guda uku a lokaci d'aya!" Yadda take fad'ar maganar muryar ta rawa take yi kana ji kasan cikin tashin hankali da d'imauta take. Baza ka d'auka akwai halitta a wajan da take ba saboda yadda wajan yake da duhu sosai, aci balbal d'in a farkon wajan take kana shiga ciki babu haskenta. "Ha!Ha! Bana fad'a miki daman zata haihu ba?. Mun riga mun ga haka zata haihu kuma y'ay'an za su girma." Ya fad'a cikin murya mara dad'in sauraro mai bada tsoro da firgita wanda yake sauraronta. Abin mamakin bata tsorata ba sai sake gyara zama da tayi tace, "Ya zanyi? Bazan iya jurewa hakan ba ko kad'an, ka nema min mafita kaine k'arfin guiwata. In y'ay'an nan suka girma na shiga uku.""Me kike so a yiwa yaran?, A kashe su? A haukata su?, A lalata rayuwar su ta gobe?, A juyar da tunanin su?, A sace su?. wanne kike so ayi musu a ciki? Ko wanne kike so zamu taimaka miki."D'aure fuska tayi alamun rashin imani ya d'arsu a zuciyarta cikin kakkauasar murya tace, "Bana so a kashe su; ina so su rayu su d'and'ana irin kalar rayuwar da na tanadar musu, bana so su haukace saboda so nake da hankalin na su amma su kasa sarrafa shi, bana so a lalata rayuwarsu domin da nutsuwar su nake buk'atarsu, bana so a sace su; domin a gidansu nake so su tashi inda suna ji suna gani su da gidansu sai bare ya fisu daraja da mahimmaci a cikinsa. Ina so su rayu amma ko wannensu asan abin da za'a saka masa wanda dalilin hakan suna ji suna gani sarautar zata fi k'arfinsu nan gaba. Bana son jinin Rabi yayi wani ƙwaƙwƙwaran motsi sai na so, bana son jinin Rabi ya d'aukaka a duniya, yadda take jin tafi kowa ina so na nuna mata ita ba kowan komai bace face farcen susa a wajena."Ya kuma sakin dariya mai munin sauraro yace...
Contents
Table of contents
Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.