KULLALLIYAFree

ArewaPen original

AdventureFreeOngoing

KULLALLIYA

  • 1views
  • 27chapters
  • 0audios
  • words
  • 0likes
Start reading

Share:

The story

Synopsis

ongoing

No synopsis yet.

About the author

An educator, classroom instructor, a writer, an artist, a fashion designer, I love creativity...

More from @ummufarhaanah143

Sample · The tragedy of my life

******KULLALLIYA******NA SAFIYYAH ABDURRAHIM ABUBAKAR (UMMU FARHANAH)...1...Rayuwa takanzo wa bawa cikin yanda mai kowa da komai ya tsara abinsa, duk yanda kaso da kiyaye kanka abu ne mawuyaci, yanda na tsinci kaina cikin rayuwata ni kaina na san babu yace zanyi, ni din bani da wani gata sai yanda akayi da ni, uwa uba bani da wani tushe da zan danganta kaina dashi, irin haihuwar da uwata tayi mani ya sanyani zama "celebrity" yanda ba dama in ratsa guri yanzun zakiga ana nunani mutane suna fadin gata nan, aibatani kam har ya zame mani jiki tunda ba yau aka fara ba, abin da kan sosa mani zuciya har zuwa wannan ranar babu tsayayyar magana game da asalina, Allah yasa ni ba 'yar gaba da fatiha bace, na fadi ina share hawayena babyna ta fadi cikin yanayin daga murya tana dan duduba inda zata hangoni,ta dan 6ata rai sannan naji tana fadin ke kuma ba'a isa a taka maki burki ba ko? Na girgiza kaina gami da mikewa ina gyara zaman takalmana, biyoni, ta fadi sannan ta yi gaba ni ma na rufa mata baya, mummy Rahmah kenan matar da nayi wayo da ita a matsayin uwa, duniyar nan bani da sama da ita, palon gidan muka zauna nida uwar gidan gwamnar jihar da aka maidani don tabbatar da lafiyata kafin a gama case a high court,me zakici? Tayi mani wannan tambayar tana kallona, na koshi na fadi kai tsaye, Rahma kuje please naga kece acting mummyn ta zatafi sakewa da ke, muka koma dakin da aka cika mani da abin duniya a matsayin muhallina, na zauna dab da kofar dakin ina razgar kuka mai tsima rai, a hankali ta karaso ta kama hannayena 2 gami da cewa its ok babyna me haka? kina girma kina cin kasa haka na koya maki? Na girgiza kaina amma na kasa tsayar da kukan da yaci karfina, muryarta naji tayi rauni karo na farko a rayuwata kenan da zanga raunin mummyna Rahmah, ta janyoni jikinta tana shafa mani kai sannan ta soma fadin zuciyata ta kan damu da yanayin da nake ganin ki a ciki babyna, ban son damuwarki sam amma ya na iya? Wannan itace kalmar data zame mata abin fadi a duk sanda na rikice mata,ta fice yayin da narakata da idanu zuciyata cike da abubuwan da suka min karan tsaye cikin raina, ni MATSAYINAH kawai nake son sani, ba jimawa ta shigo da plates kala kala mai dauke da nau'in abinci, tana dan yi murmushi daidai lokacin da take fadin come to me my child, na karasa na fada jikinta ina gunji, me ke shirin faruwa dake ne Hameedah? Mummy ban sani ba jiya a sch wasu 'yan class dinmu suka bani newspapers na karanta mai dauke da hotounana da labarai kala kala, mummy pls kice mani karyane Allah ke na sani ke nake mafarkin samu a matsayin uwa, bani da kowa mummy ki taimaka mu kasance tare sai dai mutuwa ta raba mu, mummy ke fa ina 'yan uwanki? Ta dan jima kafin tayi magana har nayi zaton bazan samu wannan amsar ba naji tana fadin nima bani da kowa sai ke, kaman ya? Kawayena su...

Continue reading free chapter

App exclusive

Continue “KULLALLIYA” in the app

The author limited this story to mobile. Open the app to read, listen, and keep your place.

Download on the App StoreGet it on Google Play