FreeArewaPen original
RAYUWA DA ƘADDARA
- 1views
- 102chapters
- 0audios
- words
- 0likes
Share:
The story
Synopsis
No synopsis yet.
About the author
Am so proud to be a hausa writer.
Sample · RAYUWA DA ƘADDARA Chapter 1
RAYUWA DA ƘADDARA! _©️Ayshat Ɗansabo lemu_ Ina mai farawa da yabo tare da ɗinbin godiya ga Allahu (SWT) da ya bani ikon fara wannan rubutu,sannan ina miƙa godiya ga tarin makaranta littafaina waɗanda suka yi mini uziri tare da tayani farin ciki akan ƘADDADAR ZOYA da ya zama bai kammala ga makaranta ba ,a sakamakon saye labarin da aka yi domin a juyashi ya zama film.Sannan ina muku albishir da cewa wannan labari na RAYUWA DA ƘADDARA zai zo muku da tarin faɗakarwa da ɗibin darussa na rayuwa kala-kala,domin kuwa labari ne da zai taɓa ɓangarori da dama.Sannan zai nishaɗantar tare da sanyaya zukatan makarantansa da sassanyar soyayya mai tsayawa a rai,don haka kar ku bari ayi wannan tafiyar babu ku a cikinta.Sannan kuma babban abin farin cikin shi ne, na sauƙaƙa kuɗin sayen wannan labari,duba da yanayi da ake ciki na matsewar tattalin arziƙi,domin ina ma kowa sha'awar ya shigo cikin tafiyar. GARGAƊI Wannan labari da dukkanin abinda ya ƙunsa mallakin marubuciyar ne,don haka ban amince a juya min labari ko sauya shi ta kowa ce iriyar fuska ba.Ban amince a karanta min labari a kowani kafar sadarwa ba tare izinina ba,yin hakan babban kuskure ne,don haka a kiyaye. Chapter 1 SHIMFIƊAR LABARI... GARIN ZAZZAU.Ita dai masarautar Zazzau tana daya daga cikin muhimman masarautun kasar Hausa da ma yankin Afirka ta yamma.Tarihi irin na kunne ya girmi kaka ya yi nuni da cewa, Zazzau wata daɗaɗɗiyar masarauta ce, wadda ta samo asali tun ɗaruruwan shekaru da suka gabata, wato daga lokacin jahiliyya ko kuma kafin zuwan addinin musulunci.Yadda kalmar ‘Zazzau’ ta samo asaliTushen wannan kalma ta ‘Zazzau’ yana da rassa biyu, na farko yana da nasaba da yanayin kasar ta Zazzau, wanda daga Katsinanci ke nufin ‘zo-zo’, wato kasa mai laka, ba mai rairayi ba, wadda za a iya yin shuka a kanta, kuma ta tsiro.A wani kaulin kuma ‘Zazzau’ na nufin wani takobi, wanda ja-goran jama’a yakan dauka ya jagoranci jama’a a wajen yaki. Mai daukar wannan takobi ba sarki ake kiransa ba, a wancan lokaci ana kiran sa ne ‘Madau-Zazzau’, wato ‘Mai Dauke da Zazzau’. Asalin Kalmar Zariya kalma ce da ta samo asali daga sunan Zariya ‘yar Sarki Bakwa Turunku, wadda kanwa ce ga Sarauniya AminaBambancin Zazzau da Zariya shine,Zazzau masarauta ce, wadda ta kunshi dukkan ƙasashe da garuruwan da ke bin masarautar. Zariya kuwa shi ne babban birnin da sarki yake zaune da hakimai da ’yan majalisarsa ana gudanar da mulki. Sauran hakimai da suke da kasashe suna kawo wa sarki rahoto, su kuma ana aika masu da umarni.Kafuwar Masarautar ZazzauA zamanin maguzanci, wato shekaru aru-aru da suka gabata, babu wani addini da ya shigo, sai al’adu ko rayuwa irin ta maguzanci. Da kuma ƙaura daga wannan waje, a koma wancan waje, ita ce al’adar Bil’Adama, a k...
Contents
Table of contents
Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.