FreeArewaPen original
❤️Lailerh Mansoor ❤️
- 1views
- 5chapters
- 0audios
- words
- 0likes
Share:
The story
Synopsis
No synopsis yet.
Sample · The beginning
*❤️ LAILERH-MANSOOR ❤️* ©️ Maimunatu Abdullahi*🦅M.W.A🦅*_DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN K'AI_Dis book is solely for my biggest supporter, my overall, my sisi from another mom, halak malak, Maman biyu na, khadeeja nerh I love you and I cherish u alot 🤞one love dear one love 💕I dedicate dis page to my sweetheart, favorite sis Hauwa'u (Walida) masoyiya Ya, Allah ya Miki albarka ya Baki Muhammad 🤞❤️*Maimoon* 1......._KADUNA_ Nigeria....Madaidaicin tsakar Gida ne dake d'auke da rijiya daga gefe, sai kitchen Dake rufe daga can hannun dama, daga gefen kitchen d'in akwai d'an dakali da aka zagaye da plaster inda ya kasance gurin wanke-wanke da few plates da pots a wajen wad'anda ba'a wanke ba, sai bayan gida Dake rufe Shima daga hannun hagu, d'an k'aramin falo ne da d'akuna guda biyu falle d'addaya a cikin k'ofa d'aya Dake tsakar gid'an, gidan fes- fes Babu alamar datti ko d'igo.Wata kyakkyawar macece ta fito daga d'aya daga cikin d'akuna guda biyun, matar doguwa ce dirarriya sosai Mai hasken fata, irin hasken y'an Ethiopia d'innan, a k'alla zatayi shekara 33 zuwa 35 haka, tana Sanye da Riga da zani da ya yi wa fatarta kyau sosai duk da ba wani Mai nauyin kud'i bane, bak'in hijabin jikinta ta gyarawa zama tana k'arasowa falon, ta Sami guri kan d'aya daga cikin kujeru uku da ke gyararren falon Dake k'amshin turaren wuta, cas'bah d'in hannunta ta ajiye akan hannun kujeran tare da mik'e kafafunta, masu d'auke da dogayen yatsunta masu kyau, tana tunanin shin ina Lailerh? It's already 6:00pm tasan duk inda take tana hanyar gida, tun k'arfe 5:30 ya kamata ta iso gida, wayar ta dake kan kujerar ta janyo da niyyar Kiran layinta, sallamar da taji daga tsakar gida yasa ta sauk'e ajiyar zuciya tare da ajiye wayar a hannun kujera tana amsa sallamar tare da kallon k'ofar falon da kyakkyawar murmushi a kan fuskarta, yaye labulen falon akayi ta shigo d'auke da wata sallamar kyakkyawar fuskarta a had'e Babu yabo Babu fallasa, k'ura mata ido Ammi ta yi ganin yadda take takowa a sanyaye kamar wadda k'wai ya fashe wa a ciki, dogon hijab maroon colour ne a jikinta da ya rufe har k'afafunta, socks d'in Dake k'afafunta kad'ai ake iya hangowa, hannayenta duka suna cikin hijab d'in, sai Kuma kyakkyawar fuskarta Dake d'auke da dara-daran idanunta da suka d'an canja launi saboda gajiya, sosai take kama da Ammi tsayin, dirarren jikin, kyawawan idanuwan da suke Nan farare tass, k'wayar idon Kuma bak'i sid'ik. ga gashin gira bak'i cikakke da ya ƙarawa fuskar k'awa, d'an k'aramin Baki kamar cokali bazai shiga ba gashi nan pink yirr dashi, da dogon hanci Daya dace da zagayayyiyar fuskarta, duk irin na Amminta, zuba mata ido Ammi tayi tana kallonta, komai nata Lailerh ta d'auko yatsun k'afafunta d...
Contents
Table of contents
Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.