FreeArewaPen original
AYMANA ROMANTIC STORY!
- 1views
- 16chapters
- 0audios
- words
- 0likes
Share:
The story
Synopsis
No synopsis yet.
About the author
Full house wife# Ngizim tribe from Potiskum LGA Yobe State # Living at BADE LGA Yobe state Nigeria # Also a student af computer science @ Yobe state University (YSU)# A writer of Hausa Novels.. #
Sample · Page 1
💥💥 *AYMANA.....!*💥_ROMANTIC STORY_ *MALLAKAR:-OUM MUMTAZ* ***@Oum_Mumtaz123 .*FREE BOOK.*_LITTAFIN KYAUTA._*DEDICATED THIS BOOK TO SULEIMAN A ABBA* ❤️ *PAGE 1* Misalin k'arfe 2 na daren ranar litinin,yarinya ce yar kimanin shekaru bakwai ke zaune cikin wani daki, da suka kasance su uku,sauran na baccin su, ita kuma idanun ta biyu.wanda kallo guda mutum zai yi mata,ya tabbatar da cewa a matukar tsorace take a dai-dai wannan lokacin.K'arar k'ofar dakin da taji ne yadawo da ita daga dogon tunanin da ta fada, wanda a matsayinta na mai karancin shekarun da bai kamata ace tasan ta tashi a dai-dai wannan lokacin domin yin tunani ko kuma wani abin ba!Bata gama dawo wa daga tunaninta ba, taji saukar tsumagiya mai matukar zafi da ya sa ta gantsarewa sabida azaba tana sosawa, wanda ta tabbatar wannan ba komai bane illa dorinar *ANTY* ...!!"Anty dan Allah kiyi hakuri wlhy banyi fit'sari ba,kuma banyi bacci ba kamar yadda ki ka ce kar nayi." Fadar wannan karamar yarinya cikin karamar muryarta ta yara mai cike da t'san-t'san t'soron da take ciki.Ai kuwa Anty bata sarara mata ba,saida tamata bulala kusan goma acikin wannan daren kamin tabar ta, tana sakin kwafa.Abin mamaki kuma sai naga tayi ma daya da ke cikin biyun da suke kwance k'afa! Ma'ana dai ta shure ta, wanda hakan yayi sanadiyyar farkawar yarinyar daga dogon bacci daya d'auke ta a gigice. LSai da tayi mata bulala itama, kamin tafita daga dakin tana huci, kaman wacce tayi fada da sa'anninta,ta koma wani part daban, wanda nake kyautata zaton daga nan ta bullo, kamin tashiga saida ta saita kanta kamar ba ita ba!Tana shiga bedroom din tayi tozali da *BABA* dake zaune bakin gadon dake cikin bedroom din, ta shaida masa akan ta tashe su sunyi fit'sarin! Daga nan kuma suka bi lafiyar gadon su,suka koma baccinsu.Wannan karamar yarinyar kam kuka takeyi sosai a wannan daren, dak'yar dayar ta lallashe ta wacce bazata wuce shekaru 9 ba,kamin tayi shuru.Rungume da junansu suke kwance,wanda da kyar bacci yayi nasarar yin awun gaba dasu mai cike da firgicin kar Aunty ta dawo……!K'arfe hudu asuba taji an mata wani kalar bugu mai matukar zafi da kafa, wanda hakan yayi sanadiyyarfarkawarta cikin gigicewa da rawan jiki, ba tayi mamaki ba kasancewar tasan ba kowa bane mai wannan danyen aikin face Anty. "sannu inna uwarsu matar ubansu,kedin ba cewa nayi karki kuskura ki kwanta ba ne wai dan ubanki...?"Fadar anty cikin zafin rai kamar wacce take fada da sa'arta a sanda take sakar mata rankwashi a tsakiyar kanta. "Anty kiyi hakuri wallah...
App exclusive
Continue “AYMANA ROMANTIC STORY!” in the app
The author limited this story to mobile. Open the app to read, listen, and keep your place.