FreeArewaPen original
YAR BAƘA
- 1views
- 2chapters
- 0audios
- words
- 0likes
Share:
The story
Synopsis
No synopsis yet.
Sample · BABI NA DAƳA
BABI NA DAYA(1)Zaune take a tsakar gida kan tabarma ta saka dukka hannayenta a kuncinta tana tunanin rayuwa da irin kalubalen da take fuskanta a gidan mahaifinta wanda idan ba ka sansu da dadewa ba zaka rantse da Allah cewa ba Umma bace ta haifeta saboda bayyanannen bambancin da take nunawa tsakaninta da yar uwarta Suhaila wadda ta girme mata da shekaru hudu. Sabirah ta kasance baqa qirin. Irin baqin nan me maiqo da naso kuma duk cikin gidan daga kan mahaifanta, Suhaila da qannenta guda biyu Abbas da Imam ita kadai Allah yayi wa irin wannan halittar. Gaba ɗaya danginsu za'a iya cewa babu me irin bakinta dukda cewa akwai farare, baqaqe da wankan tarwada a zuria'arsu. "Yar baƙa meye haka kin rafka tagumi kamar me takaba?" Imam, autansu me shegen tsokana ya tambayeta yana dariya."Wai Imam yaushe na zama sa'ar kane?" Sabirah ta tambaye shi da muryanta me kauri kamar ta maza. Me Ima...
Contents
Table of contents
Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.