Doctor ShazimFree

ArewaPen original

General fictionFreeOngoing

Doctor Shazim

  • 1views
  • 15chapters
  • 0audios
  • words
  • 0likes
Start reading

Share:

The story

Synopsis

ongoing

No synopsis yet.

Sample · Episode 1

*** Doctor Shazim👨‍⚕️    Daga alƙalamin KHADIJA ( M ) ABDULWAHABKAINAAT... ✍  Proud to my first novelIna alfahari da kasan cewar wannan littafi na farko agareni 📚  Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah ma ɗaukakin sarki mai kowa mai komi da ya bani ikwan rubuta wannan littafi. Ya ubangiji al'arshe kabani ikwan rubuta abin da zai amfani muslinci da muslmai, ka bani ikwan rubuta abun da zai amfaneni duniya da lahira 🙏 ✖️ ✖️ ✖️ ✖️ ✖️ ✖️ ✖️ ✖️ Ban amince wani ko wata ya yi amfani da wani sashe na littafin  nan ba ta kowace hanya, ba tare da an nemi izni a wurina ba. idan kunne ya ji jiki ya tsira!Wannan labari ƙagegen ne ,sannan ban rubuta shi ba da niyyar muzanta wani ko cin mutuncin wani ba, duk  wanda ya ga wani abu yayi shige da halayyar shi arashi ne.  Season oneFree Episode 1_2🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيمِ_12 June 2003_Ƙarfe 12:30 AmYanayin sanyin da gari yayi, da iskar da ke kaɗawa wanda ya haddasa ganyayyakin bishiyu yin rangaji, tare da ba da wata sassanyar iska. Yadda sauran ruwan saman da ƙasa bata gama shanyewa ba, da wanda yake gudu acikin kwalbatoci zai tabattar maka da lallai damuna ta kama. Shiru anguwar take sai kace ba kowa a cikin ta saboda yanayi na dare haɗi da damuna, duk da daman ba'a cika samun mutane na kai kawo a cikin irin waɗannan anguwannin ba ko da kuwa da rana ne, sai hasken bulbs daya haske anguwar haɗe dana street lamps kaɗai ake gani.Anguwace irin ta masu faɗa aji a cikin ƙasa, domin kuwa daga shahararrun yan kasuwa sai manya a gwamnati ke a cikin ta. Motace ta shararo da gudu daga kwanar dake hannun dama a cikin anguwar, yayin da wasu ba ƙaƙen motoci guda huɗu ke biye da ita. Gudu motar take sosai har ta fita daga cikin anguwar ta hau babban titi, still wa ɗannan moticin na biye da ita a bayaDaga irin gudun da mamallakin motar ke yi zaka san cewa yana gudu ne tsakanin rayuwa da mutuwa.ta mirror ɗin motar yake hangen fitilar motocin da ke binsa, yana gudu motocin na bin sa har suka hau kan titin da zai fitar da kai daga garin, gudu suke har suka fita daga garin, in ban da salati da neman ɗauki daga ubangiji babu abun da mai motar nan ke yi.domun shi a yau ya san tashi taƙare, saboda ya galabaita a dalilin dukan daya sha, tukin neman ga garar sa yake, ƙarfinsa ya kusa ƙarewa, dubawa yayi ta cikin mirror motar amma bai ga alamun waɗannan motocin ba, tunani ya fara to ko ya tsre masu ne, amma duk da haka bai fasa gudun da yake ba, wani mummunan Bugun da yaji an kaima ma motar shi ne yasa shi fahimtar ce wa kenan wata hanyar suka bi amma suna biye da shi mirror ɗin motar ya ka...

Continue reading free chapter

Contents

Table of contents

Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.

chapters15
premium0

Continue in the ArewaPen app

Unlock offline reading, audio mode, and sync your bookmarks instantly.

Download on the App StoreGet it on Google Play