FreeArewaPen original
BA MAHAUKACI BANE
- 1views
- 50chapters
- 0audios
- words
- 0likes
Share:
The story
Synopsis
No synopsis yet.
Sample · 1
KANO STATEGADAR SALGA Unguwa ce mai zaman kanta wacce take daura da kasuwar kurmi tsohowar kasuwa mai d'umbun tarihi a jahar KANO Cikin rukunin gidajen yaku bayi na cikin unguwar. Matashiyar budurwa 'yar kimanin shekaru goma sha tara Zuwa ashirin zaune a kan kujera 'yar tsuguno da tarin wanke-wanke a gabanta tana wankewa tare da kifewa a cikin wani babban kwando. wanke-wanken take tun k'arfi da alamar sauri a tare da ita.Cikin rashin kintsi! Saliha Ta iso inda take, ba tare da tunanin komai ba ta kurma mata wani irin ihu! a cikin kunnuwanta! A Zabure! ta juyo har farantin dake hannunta yana fad:uwa a kasan gurin, idanuwanta sukayi rau-rau kamar zata fashe da kuka ta fara magana cikin yanayin na 'bacin rai! tare da yanayin hallitar da Allah yayi mata tace."Saliha menene haka."?Cike da rashin mutunci tace." Yo idan ba haka akayi miki ba ai ba za kiji magana ba, yaushe zan dinga wahalar da kaina gurin kiran sunanki ai ihu! kawai shi ya cancanta ayi miki tunda kunnuwanki a toshe! suke."Girgiza kanta kawai tayi tare da mayar da kanta 'kasa tana cigaba da wanke-wanken dake gabanta.A fusace! tace."Au! Shahida mahaukaciya kika mayar dani ina miki magana kinyi min banza to bari naje na shedawa wacce ta aiko ni kiran ki.Hanci ta shak'a ta sanya hannuna ta goge gumin goshinta cikin yanayin magana irin ta kurame! tace."Saliha kina dai ganin wanke-wanken nake ko."Saliha ta watsa mata harara da fadin." To ba zaki bar wanke-wanken ba ki tashi ki je kiran da take miki ba."A hankali ta ajiye sosan dake hannunta ta mike tsaye hanya ta nuna mata da hannu da k'arfi ta ce"Wuce muje." girgiza kanta tayi rai a b'ace tayi gaba Salihan ta rufa mata baya.Baba Asabe tana zaune a tsakiyar rumfa tana d'aura gishiri su ka yi sallama Saliha kai tsaye cikin uwar d'aki ta shige tabi lafiyar gado. Ita kuwa tsugunuwa tayi a gabanta cike da ladabi tace."Baba gani Saliha tace kina kira na."Ta ajiye d'aurin gishirin ta janyo jakarta dake gefe kudi ta dauko daure a leda ta kalleta da fadin." Bakin asibiti za ki je ki dauko min man gyda tun shekaran jiya ya k'are anata zuwa nema." bakinta kawai take kallo, nan ta fahimci abinda take nufi, tunda ba wai da 'karfi take maganar ba, shiyasa ta tsirawa bakinta ido, ta na ji amma ba sosai ba, shiyasa wani lokacin idan ana magana take bin bakin mutum. nan take fahimtar komai.Cikin saurin magana da yanayi na harshenta ta ce." Ban gama wanke kwanukan ba." Ta ce."Ki ajiye idan kin dawo ki k'arasa ai da sauran lokaci." Ta amsa da "To" Tare da mi'kewa. uwar dakin ta shiga domin dauko hijabi nan taga Saliha a kwance da waya a hannunta tana game.Girgiza kanta kawai tayi ta bu...
Contents
Table of contents
Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.