Ramin muguntaFree

ArewaPen original

RomanceFreeOngoing

Ramin mugunta

  • 1views
  • 1chapters
  • 0audios
  • words
  • 0likes
Start reading

Share:

The story

Synopsis

ongoing

No synopsis yet.

Sample · Ramin mugunta chapter 1 -2

Haka MANAL ta kuma wanke kayan dik da sanyin da ake surawa, sannan tazauna zaman jiran subushe, "kee kee kee MANAL" mamy ce take ƙwalamata kira, jiki na kyarma taje ta tsuguna tace, "gani mamy" tafaɗa cikin rauna nanniyar murya dan tasan yau kashinta yabushe batagama tina ninda takeyi ba taji an rufeta da duka, ta ko ina ihuu take tanabata haƙuri amma kamar tana tinxirata ƙafa tasa taringa haurinta harseda taga ta galaɓaita sannan ta ƙyalete, zuwa wannan lokacin MANAL tajigata jitake gwara mutuwa da wannan azabar datake ciki, ƙafa tasa ta taka mata hannu wata razananninyar ƙara tasaki se kuma ɗif babu alamar rai ajikinta, "kuma wallahi kitashi kije ɗora abin cin rana ki kuma gyara gidannan dan baƙina sunkusa ƙarasowa" seta kuma harbinta da ƙafa tajuya cikin gida abinta, ahankali MANAL tasoma buɗe idonta dasuka mata nauyi tafi minti talatin da far faɗowa daga suman datayi amma takasa motsawa jitake kamar hannunta ba'ajinkinta yaje ba. tazo zata miƙe jiri yakuma ɗibarta ta faɗi tayi haka yakusa sau uku kafin allah yabata sa,a tamiƙe tana ɗingisa ƙafa, haka tashiga kicin ɗin dik da bagani take sosai ba. tajima tana girkin itace ɗora wannan sauke wannan, se la,sar sakaliya tagama sashin mamy tanufa wanda ada yake mazaunin na MOMYN ta, da sallama tashiga amma ba,a amsa ba hakan yasa ta kumayi, ZAINAB ce ta fito daga ɗakin batara da kalli inda take ba tayi gaba, ganin haka yasa itama MANAL ta fito daga ɗakin ahanya sukai karo da mamy tayi saurin durƙusawa ƙasa baki na rawa tace "mamy nagama girkin koda wani abinda za,ayi?" wani matsiya cin kallo tabita dashi kana tace, "au sokike in kuma mai maita miki to canayi ki gyara ko ina na gidannan", sunkuyar dakai MANAL tayi hawaye na bin kun *** cikin tsoro da gudin abinda zeje yadawo tace, "dan mamy kibani abinci yinwa nakeji yau kwana na biyu banci komaiba""ehhh lallai yarin ya kingiga ina magana kina cewa abinci zakici shegiya acici to bazakici ba maza maza kitashi kiyi abinda nace miki" ta faɗa cikin tsawa jiki na ɓari, MANAL ta tashi har tana neman faɗowa daga matattakalar benana, haka ta gyara gidan tanayi tana faɗuwa sabida yinwar dataci ƙarfinta, dakyar tana gamawa taja jiki dakyar tashige ɗakinta, sallah ma azaune tayi ta, ta ɗan kishin giɗa. nantake wani azababben bacci me haɗe da yinwa yayi gaba da ita tarada wasu muna nan mafarkai, tayi nisa cikin baccin da bawani daɗinsa takeji ba taji ankwara mata ruwa me sanyi kamar daga cijin fireza aka cjroshi.tini jikinta yahau tsuma ta takure guri guda kamar tsumma., wata wulaƙan tacciyar dariya ZAINAB tayi tana kallon yanda haƙoran MANAL suke gwaruwa kamar mazari ''shigiya me suffar aljanu kawai sekizo DADY na kiranki yau kam sekin ƙwammace ƴan fashinda suka kashe iya yanki kema sun haɗa dake" daga haka ZAINAB tajuya tana sakin wani shu,umin murmushi, MA...

Continue reading free chapter

App exclusive

Continue “Ramin mugunta” in the app

The author limited this story to mobile. Open the app to read, listen, and keep your place.

Download on the App StoreGet it on Google Play