FreeArewaPen original
RANAR NAKA...
- 1views
- 21chapters
- 0audios
- words
- 0likes
Share:
The story
Synopsis
No synopsis yet.
About the author
Marubuci ba makaryaci ba ne
Sample · Chapter 1
*RANAR NAKA..NAMARYAM IBRAHIM LITEE1Amatu! Amatu! Amatullahi" muryar dattijuwar ta karade tsakar gidan, wata yarinya yar shekaru bakwai ce ta fito tana amsawa "Inna ina bandaki ne" ta fadi tana ajiye butar hannunta sai ta karaso gabanta da sauri tuwo ta nuna mata da ta kwashe yana tururi "Ga abincinku can ke da Sumayya kai muku daki " ta ce "To Inna" ta dauka ta wuce dakin, dakin ginin kasa ne, kasan dabe ne gadaje biyu ke ciki babban gado mai rumfa sai karami shi ma na karfe . Gefe daya budurwar me amsa sunan Sumayya wadda kanta ke kasa tana rubutu Amatu ta isa gaban ta ta ajiye kwanonin "Yaya Sumayya ga abincin mu in ji Inna" a hankali ta dago kai tana kallon tuwon dawa da miyar kubewa danya a yatsine ta ce "Wannan tuwon shi ne abinci? Ta maida kanta ta ci gaba da rubutunta. Amatu ta fita ta dauko faranti ta dawo dakin ta debi tuwon ta zuba miya ta zauna ta shiga ci tana jin dadin abincin har kunnenta, tuwon jar dawa ne wadda aka surfa tayi danko kwarai miyar kuma tayi yauki ga manshanu ta sha, ta gama ta fitar da kwanonin daidai nan mahaifiyar ta su me suna Abu ta shigo dakin, ta kammala hidindimunta na tsakar gida tayo wanka hade da alwalar La'asar ta dubi yayanta Sumayya na ta rubutunta Amatu na yan wake waken su na yara ta ce "Sumayya ba ki ji kiran sallar La'asar ba? Ku hanzarta tashi maza ku yi Sallah ku tafi islamiyya". Suka amsa da "To Inna" uwar ta kabbara sallah su ma suka yo alwala suka fara sallar, da idarwar su Amatu ta sanya uniform na islamiyyar, amma Sumayya sai da tayi wanka ta tsala kwalliya kamar mai zuwa biki sannan ta sanya uniform, kowa ya dauki jakarsa suka yi ma Innar su sallama. Suka fito sun dan yi nisa Sumayya ta ce ma Amatu "Ni fa Amatu ba za ni Islamiyyar nan ba, tun ba ka da wayau kake zuwa islamiyar nan, a ce har yanzu shekaru sha bakwai da girma na ma sai na je? gidan Rabi Lawal za ni idan an tashi ki biyo min sai mu koma gida" Amatu ta dube ta "Amma yaya Sumayya ita makarantar boko kullun sai kin je amma islamiyya sai ki ki zuwa ki ce kin girma". Kallon mamaki ta bi kanwarta ta da shi ganin yar shekaru bakwai ke ga ya mata haka, kafadarta ta dafa "Kin ga ita boko idan ka yi ta za ka waye ka goge ka samu miji me kudi ka aura, amma ita islamiya da zaran ka samu yanda za ka yi Sallah ai shi kenan" yarinyar ta dan bata rai "Ba fa shi kenan ba yaya Sumayya Malamin mu ya ce ka nemi ilimi tun daga zanen goyo har....... "Dakata dakata! Amatu ta katse ta "Ni dai yanzu ba waazi na ce ki yi min ba, wuce ki yi tafiyarki makarantarki, ni na girma na daina zuwa, amma kar ki fada wa Inna ko Baba kin ji Amatu na?...
Contents
Table of contents
Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.