SILAR MUTUWAFree

ArewaPen original

HorrorFreeOngoing

SILAR MUTUWA

  • 1views
  • 10chapters
  • 0audios
  • words
  • 0likes
Start reading

Share:

The story

Synopsis

ongoing

No synopsis yet.

Sample · Chapter 1-2

*💔🧟‍♀️☠️SILAR MUTUWA🧟‍♀️☠️*💔        (Horror Story)     ZAHRA ROYAL STAR CE.......✍️*DA SUNAN ALLAH MAI RAHMA MAI JIN K'AI*PAGE 1️⃣➡️2️⃣*Federal University dutsinma*Wata y'ar madai-daiciyar mota ce ta tsaya cikin filin school d'in bud'e marfin motar akai cike da takon k'asaita take ta fito daga cikin motar bak'in gilas d'in dage manne da fuskarta ta cire tana bin school d'in da kallo kasancewar zuwanta ne na farko.Can ta tsinkaye wata murya na faman kiranta cike da murna taji an rungumeta da sauri ta waigo tana yamutse fuska da sauri ganin yadda duk suka rirrik'eta ta k'ara b'ata fuska ta ce "wai Bilki dake da Nawwara wai yaushe zaku canza ne shi yasa fa ban so zuwa school d'aya daku ba shi yasa again na ce ku fara yo gaba nabi bayanku shine daga isowata duk kunbi zaku wani kada ni", ta idasa maganar tana k'ara bin school d'in da kallo yadda taga duk Arna sunyi yawa a cikinta da sauri Nawwara ta d'an saketa ta ce "kai Surayya kefa akwai yarfa mutum wallahi mufa murnar zuwanki ne yasa kinga bamu san kowa ba a cikin school d'in nan", Bilki ce ta amshe da cewa "kai gaskiya Surayya daba dan mu k'awaye bane tun na yarinta da tuni mun barki da halinki akwai ki da murd'and'an hali".Ganin kamar sunyi fushi yasa Surayya cewa "kufa dad'i daku akwai saurin fassara mutum nidai kun sani sai kuna hakuri dani school d'in ce kamar b'ata kwanta min a rai ba", ta idasa maganar tana tafiya kamar ba ita tayi maganar ba ganin tabi wata hanya yasa da sauri Nawwara ta ce "Surayya ki tsaya ba'a cika bi ta wannan hanyar bafa tana da matsala", d'an dakatawa tayi da tafiya tana waigowa ta ce "to sabon salo ai na ce dai ana bi dai ko kuma zata iya kaini a inda nake so ina ce hakane?", d'aga mata kai sukai cike da d'an tsoro Bilki ta ce "dan Allah Surayya kiyiwa Allah karki bi ta wannan hanyar akwai tantiran makaranta dake zama ta wajan nan duk school d'in an sansu kuma ana tsoron su ba wadda bai san tarihin su ba".Surayya kuwa tsaki taja tana ci gaba da tafiya tana cewa "zan so jin tarihin mi suka aikata har ake jin tsoron su, to daga yau za'a sake kafa wani tarihin cewa ga wadda bata shakkar kuwa dan banga wadda ya isa ya hanani zaga ko ina ko shiga wani waje dage cikin school d'in nan ba indai zuciyata taso hakan", ta idasa maganar tana shan wata kwana da sauri su Bilki suka rufa mata baya suna mamakin rashin tsoro da kafiya irin na Surayya.Koda tasha kwanar idonta ya gane mata dan-dazon maza sun kai su bakwai sai zuk'ar sugari suke zuciyarta ta buga dumm dammm dakewa tayi tana tafiya irin ko a jikinta tana niyar wuce su da sauri wani cikin y'an iskan dake zaune wajan ya ce "Oga Goga ga wata mai rabon shan duka ta biyo da hanyarka miya kamata muyi mata danna tabbata an sanar da ita waye kai", ya ida...

Continue reading free chapter

App exclusive

Continue “SILAR MUTUWA” in the app

The author limited this story to mobile. Open the app to read, listen, and keep your place.

Download on the App StoreGet it on Google Play