FreeThe story
Synopsis
No synopsis yet.
Sample · KULUWA SHAFI NA FARKO
KULUWANA ZEE YABOURDA SADIYA NASIR DANSHAFI NA FARKOGarin yayi sanyi da ni'imtaccen iska kasancewar lokaci ne na damina, shukoki koraye da bishiyoyi ne zagaye da wurin wanda suke kada iska mai daɗi. Zaune take kan ɗaya daga cikin duwatsun dake bakin tekun ƙafafunta cikin ruwa, hannayenta ta ware su tana ɗibar ruwan tana ɗan watsawa tana wakokinta na dandali. wuri ne da take samun natsuwa da nishadi da son keɓewa don babu hayaniyar mutane, mafi akasarin lokuta nan take zuwa ta zauna musamman lokutan damuna tana shak'ar iska mai daɗi da sanyaya zuciya. Hadarin da ya soma gauraye sararin samaniya garin ya fara duhu ya sata zame ƙafafunta daga cikin ruwan, Tana gyara babban ɗan kwalinta ta ware sa ya sauka saman kafadarta, Ta tashi tsaye tana ɗaga manyan idanunta tana kallon sararin samaniya, ganin hadari ya haɗu sosai ruwa na gaf da sauka yasa tayi murmushi ta furta "Allah ka bamu dami...
Contents
Table of contents
Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.