YANKAN ƘAUNAFree

ArewaPen original

RomanceFreeCompleted

YANKAN ƘAUNA

  • 1views
  • 88chapters
  • 0audios
  • words
  • 0likes
Start reading

Share:

The story

Synopsis

completed

No synopsis yet.

Sample · 1

*YANKAN ƘAUNA..!!*🌹          *NA**AUTAR MANYA*ADABI WRITTER'S ASSOCIATION           *001*Birgima take tayi a ƙasan ɗakin su wanda bai sami arziƙin ledar ƙasa ba Hannunta dafe da Cikinta Idanun nan nata sun Kumbura sunyi luhu luhu fuskarta tai jajir Musamman saman Hancinta abin ka da Tubarkallah fara ce jajir kamar ka taɓa ta Jini ya fitoSedai tsabar Rashi da Ƙuncin rayuwa yasa daidai da sutturar Jikinta idan ka kallah dab take da aga jikinta sabida yadda kayan suka Koɗe suka jeme wahala Sosai ta bayyana ga kayan na Jikinta wanda atamface amman tai shara shara kamar zata yage sedai a wanke take tas tsaf tsaf se ƙurar Ƙasar data kwasa wadda take kwance ne a ƙasan simintin ɗakin."Yaya Cikin naki? amman kina jin lafawar ciwon ko bari na leƙa ko mai chemist ɗin can ya fito na kira shi ya duba Ki seya baki magani" "karki kiramin kowa ina jin marata kamar zata Ɓalle wayyo Hajiyata"Hawaye Ummi ta share dama sun saba shiga wannan tashin hankalin Duk ƙarshen wata idan Sa'adah zatai period."To haka zaki yi ta Zama da ciwo Sa'adah ai dole inje wajan Mai Chemist ɗin can koya fito tunda shike baki magani se yazo ya ganki sabida ɗazu suman da kikai ya ɗaga mini hankali Ni kaɗai naita ihu agidannan wallahi su Umma Radio suka kunna damma kada suji Ihuna"Cewar Ummi.Sa'adatu ta cije baki tana Lumshe idanunta da suka ƙara Girma Fuskarta tai jajir musamman saman hancinta daya koma kamar Tumatur sabida ja abin ka da farar fata.Kwantar da kanta tayi ajikin Ummi tana jan ajiyar zuciya hannunta guda takai saman Cikinta tana Jin yadda mararta ke ƙara ɗaurewa Jita ke dama akwai abin da zata sha wanda ze Lafa mata wannan Ciwon dake takurata a wannan Lokacin ba wai Kukan marar kaɗai take yiba harda Kukan talauci mai za'ayi da rashi abin da kake tunanin ka gagare shi Yazo kai ya gagare ka.Baccine ya ɗauketa Ummi ta zame ta Tasanya mata ƙaramin matashi akanta Ummi uwar ɗaka ta shiga Gaba ɗaya Hajiyar su ta ɓata jikinta kasancewar tana da lalurar Shanyewar ɓarin Jikinta."Ya salam Hajiyarmu Ki min afuwa banzo na gyara ki ba abinne yayi Mini yawa"Ummi ta faɗa da ƙarfinta ta ɗaga hajiya ta jinginar da ita ajikin bango ta soma cire mata zaninta wanda ya ɓaci ta fita dashi tsakar Gida a bakin Rijiya ta aje cikin bawo ta ɗibi ruwa a buta ta shiga uwar ɗakin Wanke wa Hajiya jikinta take tana zuba ruwan a wani ƙaton Bawo wanda suke yiwa Hajiya wanka aciki to yau basu sami Damar Yi mata wankan ba sabida Ciwon sa'adah Gashi kuma ba Ruwan ɗumi Dan yau har Kitso sa'adah tai Niyyar taiwa Hajiya to Kuma se Ciwon marar ta dake tashi duk ƙarshen wata ya tayar mata shiyasa gaba ɗaya basu da Nutsuwa.Ummi ta kammala wanke wa Hajiya Jikinta ta ɗaga Bawon da Butar ta Fita tsakar gida."Kan uba!...

Continue reading free chapter

App exclusive

Continue “YANKAN ƘAUNA” in the app

The author limited this story to mobile. Open the app to read, listen, and keep your place.

Download on the App StoreGet it on Google Play