FreeArewaPen original
NI DA YAYA ARMAN
- 1views
- 15chapters
- 0audios
- words
- 0likes
Share:
The story
Synopsis
No synopsis yet.
About the author
proud to be Writer
Sample · 1_2
🍏 *NI DA YAYA ARMAN*🍏 Hot love story♥️🔐```MALLAKAR``` *Hajara L Sadeq* ~Marubuciyar~Komai mukaddari neK'addarar soyayya ta Najmat Abiy And now*NI DA YAYA ARMAN*📚 *JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION* 📚*GODIYA* godiya ta tabbata ga Allah (S W T) tsira da Amincin Allah su tabbata ga Annabi Muhammad(S A W) da ahalinsa da sahabbansa ina Godiya Ga Allah (SWT) da ya k'ara bani ikon fara rubuta littafin nan yanda na farashi lafiya ya sa na gama lafiya cikin yarda da amincewarshi.*GARGAD’i* ban yarda wata ko wani ba su juyamun Littafi ta kowace sigaba muddin Hakan ta faru zan d'auki mummunan mataki.Littafin nan NI DA YAYA ARMAN k'irk'irarren Labari ne Idan yazo daidai ko yayi shige da labarinki kiyi hakuri arashi ne.*DEDICATED TO SISTER LEMART L SADEQ*Y'ar uwa,Masoyiyata,Aminiya,Besty love Bazan tab'a iya misalta soyayyarki a cikin zuciyata ba Allah ya barmu tare my y'ar uwa Rabin jiki littafin nan gabaki d'ayanshi sadaukarwace gareki ki kiyi yanda kikeso dashi 💃💃💃💃23/May/2022بسم الله الرحمن الر حىم*BOOK ONE*📔🅿️.........1&2```Kano state```~Nasarawa Quaters~Tsit kakejin unguwar tayi shiru kasancewar ranar da ake gallawa kowa ya na gidajensu Unguwace ta y'an gayu yawaicin masu kudi sunfi zama unguwar gidaje ne na alfarma Chan na Hango wani tafkeken gida mai matuk'ar kyau da tsaruwa da kuma girma na ban mamaki Dan gate din gidan kanshi zai d'auki sama da mota sha biyar gidan gida biyu ne na kusa dashi Shima yana da kyau daidai misali Shima da gate d'inshi amma kuma akwai kofa wacce daga cikin gidan zaka bulla d'ayan gidan ba tare da kasha wahalar zagayawa ba cikin gidan ya hadu komai cikin tsari.Zaune take ta na guga ta na yi ta na Jan tsaki Inna dake zaune ta na taunar goro ta ce "da yake uban wani ya sanyaki gugar da zaki zauna tun d'azu kina yiwa mutane tsaki aikin b'urut inji tusa" Aira da a cike take daman cike da jaraba ta juyo ta ce "waike inna ina ruwanki dani ne,dandai neman tashin hankali irin naki magana nayi maki ne Dan ayi maki magana ki ce anyi maki Rashin kunya kije ki hada mutum da Abba ni kibarni da gajiya ta ma ta isheni"da ruwana dan ubanki shegiya mai kama da Aljannu figai figai kamar kaza amma sai Rashin arziki cike da ciki" tsaki taja tare da cire gugar ta mik'e tana hada kayan gugar ta ce ."Kindai kusa mutuwa mu huta " Inna cike da masifa ta dauki pillow dake kusa da ita ta jefa mata tace "uwarkice Rahama zata mutu Dan ubanki Da gudu Aira ta yi waje ta na Dariya Dan tasan yau ta tabo inna Dan ba abunda ta tsana irin kace za ta mutu. Ta na fitowa ta na Dariya sai sannan na k'are mata kallo Fara ce Sol farin nata har wani yellow yellow yake doguwace daidai misali sannan bata da k'iba siririyace amma ba Chan ba Dan tsawonta ne ma yasa za akirata da siririya badan haka ba ta na da kibar ta daidai gwargwado,ta na d...
Contents
Table of contents
Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.