FreeArewaPen original
WANKA DA GARI...
- 1views
- 22chapters
- 0audios
- words
- 0likes
Share:
The story
Synopsis
No synopsis yet.
Sample · Chapter 1-2
*** antaya cikin group ɗin da za a cigaba da posting.**ƊANƊANO! ƊANƊANO!! ƊANƊANO!!!*_Littafin Wanka Da Gari labarin Sakinaa zai cigaba da zuwa daga ranar 1/1/2024 da yaddar Allah. Littafi ne na marubuciyar zamani, ɗaya daga cikin Gawurtattu uku Fatima Sunusi Rabi'u wato Ummu Affan ɗin ku, wacce ta rubuta muku MU GANI A ƘASA... SANDAR MAKAUNIYA... CIKIN WAYE? NI DA YAYA LAMIR, FATUTU Da sauransu, a yau ma tazo muku da wani sabon labarin mai suna WANKA DA GARI Wanda take sa ran ku karɓe shi fiye da na baya, bazan zamo ɗan magori mai wasa kan shi ba. Ku dai kun san Gawurtattu uku ba sa labarin banza, kai tsaye domin magana da marubuciyar ***._*Zaku iya zuwa kuyi following ɗina a shafukana.*_Instagram_ummu-affan-writer_Facebook_Fatima Sunusi Rabi'u_Arewabooks_UmmuAffan_Bakandamiya_FatimaRabiu_Okadabooks_UmmuAffan_***_UmmuAffan_Gawurtattu uku 2024._WANKA DA GARI...©FATIMA SUNUSI RABI'UUmmu Affan*Fatan alkhairi ga ƙanwata ta gaban goshi Dr Maryamah Ibrahim Sokoto, ina miki fatan alkhairi a ko da yaushe, Ubangiji Allah ya baki miji na gari ya albarkaci rayuwarki.*_Gargaɗi da babban murya, ban amince a ɗaura mini littafi a ko wacce kafa ba, musamman masu youtube channel kar a fara ba tare da izinina ba, duk mai buƙata ya mini magana a dukkan littafina ina ajiye lamba, don Allah kar a fara domin bazan lamunta ba._*Book 1 Page 1-2*_Unguwar Rimi Kaduna State.__2015_Zaune ta ke a gefen makeken gadonta hawaye ne wasu ke bin wasu a kan kyakkyawar fuskarta, ta ra sa dalilin me yasa Abban Yusra ke mata wulaƙanci, rabon da ta gan shi yau kimanin wata biyu kenan. Me ya ke nufi da irin wannan wulaƙancin na rashin kwana gida?Wayarta da ke gefen gado ta ɗauko, lambarsa ta danna wa kira, ringing ta ke amma har ta ƙarati ɓurarinta ta gama ba alamun za'a ba ta agajin gaggawa, kira na biyu ma haka tayi sai a na uku ya ɗauka. Tun kafin ta maganantu ya riga ta cewa, "Waike wacce irin mayya ce? Na ce ki daina kirana amma kin ƙi! K so ki ke sai na saɓa miki?" Cikin sanyin murya ta ce, "Haba Abban Yusra me ya sa ka ke mini haka? Kar fa ka mante da Sakinarka ka ke magana." "Sakinaa ki kiyaye ni tun kafin ranki ya ɓaci." Ya furta a ƙufule."Tun yaushe kuma? ai raina tuni ya ɓaci, ka tausayi mini Habibi."Dogon tsaki ya ja tare da yanke kiran.Miƙewa Sakina tayi cike da ɓacin rai, A fili ta furta "Me ke shirin faruwa da ni? Me na maka ka ke son ramawa ta wannan hanyar, wanne irin zunibi ke bibiyar rayuwata har haka?"Mayafinta da key ta zara tayi waje da sauri, moto ta ɗauka tayi mata key ta fita a sittin har Baba Maigadi na cewa,"Yau me ke damun uwar ɗakina? Duk inda zaki Allah ya kai ki lafiya."Kai tsaye gidan Hajiyar Abban Yusra ta nufa, tana zuwa tayi hurn me gadi ya buɗe mata katafaran gate ɗin gidan ta tu...
Contents
Table of contents
Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.