FreeArewaPen original
DAGA MAKWABTAKA
- 1views
- 1chapters
- 0audios
- words
- 0likes
Share:
The story
Synopsis
No synopsis yet.
Sample · Book One : 01
😭DAGA MAKWABTAKA😭# Non fiction# Soyayya # Silar ƙaddarata # Cin mana/yaudarar# Zamba ci kin aminci # Cin amanar makwabtaka BA KAGAGGEN LABARI BA NE. LABARI NE DA YA FARU SANNAN BAN YARDA A CANZA MIN LITTAFI NA TA KO WACE SIGA BA, KO KARANTAR SA DAGA SHAFUKAN SADA ZUMUNTA KAMAR SU YUTUBE... KO GIDAJEN RADIYO BA DA IZININA BA. #HISTOIRE VRAIE ED. AOÛT 2023 HISTOIRE ÉCRITE PAR: Amysherh ✍️ Yanda na fara rubuta labarin nan lafiya Allah kasa na gama shi lafiya, ya Ar Rahman ka bani ikon rubuta abinda zai amfani al'umar Musulmi baki daya, inda na kuskure Ubangiji ka yafe min 🤲🤲BISMILLAHIR RAHMANIR-RAHIM PREMIÈRE PARTIE: N°01 ZAYYA Babban gida ne share kal-kal sai kyalli yake ba datti ko kadan ga shuke shuke daga ko wace kusurwa ta gidan ga kuma wani katon iccen lemu kore shar da shi a tsakiyar gidan wanda ya kara wa gidan kyau sosai. Gidan ne na masu rufin asiri sosai dan ya hadu daga mashiga babban kofa ce wanda zai sada ka da dakin samarin gidan wato su Hisham hakama idan ka dan shigo ta daman ka zaka samu banɗaki gaba kaɗan kuma dakin maigidan ne wato Abba idan ka kara gaba kuma babban falo ce dauke da ciki daya da toilette na matar gidan daga hagu kuma zaka samu dakin yan matan gidan wato dakin su Zaïya. Gaban shi kadan kuma kitchen ce share kal cike da kayan abinci daga bayan dakin su Hisham kuma garke ce ta raguna manya biyu a share ita ma sai abin cin su dake gaban su. Ku san karfe 8h45 na safe kokowa take dan neman kowace kanta dalilin an danne mata wuyan ta an kuma shake ta sosai ta yadda baza ta iya ko da kwakkwaran motsi ne dan kwatar kanta ba. A bin al'ajabin ma har kawo yau bata taba sanin ko da wa take kokowan ba saboda kullum ta kan yi irin wannan kokowa ne a duk sanda ta kwanta barci amma har kawo yau bata taba iya ganin fuskar abin fadan nata ba. Sannan bata iya ganin komai nashi sai iya hannun da ake ta son danne wuyan ta, ita kuma sai ƙoƙarin neman kowace kanta take da iya ƙarfin da Allah ya bata. Amma kash abin kamar da wuya dan ita ji take ma kamar ba da mutum take wannan wahala ba dan duk tabi ta jige da zufa ga uban nishin da take da kuma burma ihun da take duk a banza tunda ba me jin ta bare ta sa ran wani zai kawo mata dauki ko agajin gaggawa. Gashi kara jin ta take kamar duk jikinta ba rai dan kama daga babban yatsun kafarta zuwa kan ta duk ba wani amfanin da suke mata kai hatta da ɗan karamin yatsar ta na hannu ya gagare ta ta daga shi. Amma ...
Contents
Table of contents
Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.