FreeArewaPen original
K'ANGIN RAYUWA
- 1views
- 20chapters
- 0audios
- words
- 0likes
Share:
The story
Synopsis
No synopsis yet.
Sample · EPISODE 1
*K'ANGIN RAYUWA* *(THREE 3 LOVER'S FROM ROYAL STAR)* *ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION* SHARE FISABILILLAHI ZAHRA ROYAL STAR ****EPISODE* 1FACHANKAN wani K'auye ne dake k'aramar hukumar Jigawa, rayuwar K'auyan abun sha'awa ce, sai dai suna da k'arancin addini harda ma na boka, bawai babu Makarantun ba, a'a sunfi ba sana'arsu mahimmanci, da yawan y'an matan garin talla suke yi, sai kaga budurwa tana tallar abinci da dai sauransu, sana da kin kai shekara sha uku ko hud'u za'a fara shirye-shiryen aurar dake, da yawansu suna durkusar da yaransu, sai kiga yarinya k'arama ta tsofa da wuri, gara ma mazan garin idan suka dage suka gama secondary, tofa shikenan yaro ya gama karatu, wasu iyayan su tura yaro neman kud'i Kudu ko sauran garuruwa, ko a kai yaro almajiranci.Kai tsaye mu kutsa cikin labarin.Haka ce take kasancewa a gidan Alhaji Sani Mai Goro, Baban gida ne wadda ya kasance ginin k'asa ne mai d'auke da d'akona Takwas, ko wanne d'aki da akwai mamallakinsa, Sani mai Goro yana da mata uku, Inna Suwaiba, sai Inna Khande, sai kuma Inna Indo, Inna Suwaiba ta kasance macece mai son kud'in tsiya bata da hakuri dan duk wadda ya tab'a ta gidan sai an jisu tana y'ay'a biyu Hamza, sai Binta, wacce tayi aure wajan K'auyan, sai ko Inna Khande, ita bata shiga harkar kowa a gidan da wuya ana abu a gidan ta tanka, idan ba an tab'o yaranta ba, yaranta uku Ismail, wadda suke kira da Ilo, sai Sule sai kuma Abubakar, wadda suke kira da Abu, Inna Indo kuwa y'ar rigima ce itama ga habaicin tsiya, ko baka tab'a ta ba idan tasu sai kunyi rigima da ita, itama tana da yara biyu Iro, sai Mamman.Cikin yaran nasu Iro dana mata d'aya, Sa'ade da yaron ta namiji wadda ya fara zama saurayi, mai suna Hamisu, Hamisu baya jin magana son matan tsiya ne dashi kamar mi ga bin matan banza tun yana k'arami yaso ayi mai aure, saboda muguwar sha'awar da yake da ita, iyayan sunki mai auren sunce sai yaje neman kud'in idan ya dawo yayi auren shine ya fetsare yak'i zuwa neman kud'in, ya tsaya a gari a jan magana.Sai kuma matar Mamman mai suna Maryama macece itama makirar gaske baka gane gabanta bare bayanta, duk abinda take ciki da ita sai yaranta mata su biyu, Bishira da Habiba suma basa jin magana ga rashin kunyar tsiya ba wadda suka ragamawa a cikin gidan koda kuwa Kakanin su ne, wadda suke d'an shakkarsa shine Kakansu Sani mai Goro.Sai ko Abubakar shi yana da Mata d'aya shima mai suna Hadiza, itama dai y'ar rigima ce ga cika bakin tsiya, idan ta ganka da abu tofa ta kama jin haushi da hassada kenan itama sai taga tayi irinsa, tana da d'iya mace guda d'aya duk duniya tana son Na'ima ta d'ora burin duniya akan d'iyar ta Na'ima, saita auri mai kud'i kuma a birni, bata cika shiri da matan gidan ba.Sai kuma sule wadda y...
App exclusive
Continue “K'ANGIN RAYUWA” in the app
The author limited this story to mobile. Open the app to read, listen, and keep your place.