FreeArewaPen original
RANAR NAKA SAI NAKA...
- 1views
- 78chapters
- 0audios
- words
- 0likes
Share:
The story
Synopsis
No synopsis yet.
About the author
Marubuciya... In za ka fad'i fad'i gaskiya, komai taka ja maka ka biya.
Sample · Chapter 1
Duk da yadda ƙofar ta kasance ta bature mai masifar tsada, irin mai taushinnan sosai da ko an buɗe ba ta ƙara, daga yadda ta murɗa hannun ƙofar da ƙarfi, ta danno a haukace kuma a fusace, sai da ƙofar tayi wata siririyar ƙara mai kama da fitar iska. Hakan yasa mazauna ɗakin waiwayowa da sauri suna kallonta da wani yanayi mai kama da maɗaukakin mamaki a fuskokinsu.Ganin irin kallon da suke mata yasa ta ƙara harhaɗe girar sama da ƙasa tayi murtuk! Kamar an sheƙawa ƙullun kunu tafasassasshen ruwa. Kallon huɗu saura kwata ta watsa musu gaba ɗaya, sannan ta ba iska ajiyarsu ta hanyar jan tsaki ƙasa-ƙasa. Ta taka kai tsaye ba tare da tsoro ko fargaba ba zuwa gurin mamallakiyar ɗakin da take zaune kan kujerar gaban madubi, da kakkausar murya ta ce "Abincin Innaye da aka manta da wanzuwarta a cikin gidannan na zo karɓa..." "Ke dabbar ina ce ƴar ƙauyen-ƙayau da bata san abinda ya kamata ba? How dare you da za ki shigo min ɗaki kai tsaye da wani ƙazamin jikinki ba tare da neman izini ba ina tare da abokan aiki na?"Ta katse yarinyar da maganganun cikin fushi. Da miƙewarta tsaye a fusace, da ɗaga hannu ta kai ma yarinyar wani mahaukacin mari baza'a ce ga wanda ya riga wani ba.Cikin zafin nama da ƙwarewa a zamiya yarinyar tayi saurin duƙawa ƙasa marin ya bi iska. A haukace ta miƙe tsaye tana haki, domin an shammaceta, a zuciyarta take ayyana lallai da marinnan ya sauka a kumatunta ta rantse da girman Allah babu abinda zai hana ta ɗaukar wannan figaggiyar matar mai shegen girman kan tsiya da wulaƙanta ɗan Adam ta nuna ma Allah sannan ta maka ta da ƙasa. Sai dai duk abinda zai faru ya faru. "Kan Uba... Ni kika mara?"Ta faɗa cikin ɗaga murya. "Me nai miki da za ki mare ni?"Ta sake jefa mata tambayar tun kafin ta bata amsar tambayar farko. A ranta take kitsa lallai ya kamata ta nuna ma matar nan halin dabbobi da jahilan ƴan ƙauye da take yawan zaginta da su. Bazai yiwu duk zagi da tozarcin da tayi mata a cikin kwanaki bakwai na zamansu a gidan ya tafi a banza ba, lallai ya kamata ta nuna mata shiru-shiru fa ba tsoro bane, gudun magana ne.Kafin matar ta amsa, ko kuma ɗaya daga cikin mazauna ɗakin ta ce wani abu ta ɗaga hannu biyu da sauri ta ɗora akai, ta fasa wani gigitaccen ihu da muryarta mai bala'in ƙara, cikin ƙanƙanin lokaci muryar yayi amsa kuwwa a ko wane lungu da saƙo na cikin gidan.Tsakanin Innaye da take zaune kan dadduma a ɗakin da aka sauke ta acan BQ tana gyangyaɗi, da Hafiz da dawowarsu kenan mai gadi ya buɗe musu ƙofar get direba yana ƙoƙarin daidaita fakin ɗin motar a tsakar gidan. Baza a ce ga wabda ya riga wani isa cikin ɗakin Bintu da ihun Zulaikha ke fitowa ba.Tana ganin Innaye da Hafiz sun shigo ba tare da jin nauyin jikinta ba kasancewarta yarinya mai garin jiki da wani irin gudu tayi gurin Innayen ta ruƙun-ƙumeta tana ƙara ƙarfin kukanta...
App exclusive
Continue “RANAR NAKA SAI NAKA...” in the app
The author limited this story to mobile. Open the app to read, listen, and keep your place.