FreeThe story
Synopsis
No synopsis yet.
About the author
Assalamu alaikum Sunana Hauwau Shafiu Lawal. Ni Marubuciya ce, Mahaifiya, and a proud scientist. Ina zaune a garin Daura, Jahar Katsina. Rubutukana are all about romance, (coz am a sucker for it, lol). So I hope you guys will sit tight, and enjoy our beautiful ride in shaa Alla...
Sample · Chapter 1
_Kaduna, Unguwar Sarki. 2019_Misalin karfe sha daya da rabine na dare, Nadiya na lafe a jikin bangon dan karamin dakinta, jikinta a dunkule a waje daya kamar kullin kaya, ta nade kafafunta yayinda ta sanya hannu ta zagaye gwiwoyinta dasu ta nutsa kanta a tsakankanin cinyoyinta. Kanta masifar buga mata yake yi kamar ana kada mata ganga. Ita kadai tasan yanayin da gabadayanta take a ciki, ciwon kan yaje mata da wani irin zazzafan zafi a cikin kirjinta daya sanya taji kamar ana mata suya ne a kirjin.Idanunta da suka kwashe tsayin mintuna suna digar hawaye, babu abinda suke mata face zafi da zugi, kada ma kuma ayi maganar yadda dakin ya dauki wani matsanancin zafi saboda yanayin garin gashi kuma babu wuta. Macece ita mai matukar dauriya, ba kananun abubuwa bane suke sanyata zubar da hawaye ba, amma a yawancin lokuta, lokaci dai kamar wannan, dauriyarta gazawa take yi. Allah kadai y...
Contents
Table of contents
Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.