FreeArewaPen original
FITILAR KWAI
- 1views
- 7chapters
- 0audios
- words
- 0likes
Share:
The story
Synopsis
No synopsis yet.
About the author
Assalamu Alaikum Welcome to my literary corner! I'm Fadila Ibrahim, Studied Bs.c Biochemistry at Kaduna State University, A writer with passion. As a writer, I believe that communicating ideas through written words requires a blend of knowledge, skills, and passion. Below a...
Sample · Chapter 01
•FITILAR KWAI• •TSAKURE• A wani zamani daya shuɗe, Da zarar magriba ta gabato kusan ko wani gida zaka riske su ɗauke da *FITILAR ƘWAI* Tun ba a fara min halitta ba na ke wahala, har tsahon watanni biyu a cikin ciki ina gwabzawa tare da mahaifata, ni ne ƙwan halittar dake cikin ta,ƙwan halittar da ake son a zubar. Kaifin kwakwalwar da Allah yayi ma jarirai ya sanya na ke fahimtar cikin labaran ta akwai rina a kaba. Mahaifiya ta ta shiga halin tsaka mai wuya, ta sha gwagwarmaya a rayuwar ta don kare ni daga magungunan da Abba na ya ke kawo mata don zubar da ciki na, Abba ya manta cewa mugun nufi, baya kashe ɗan barewa kuma da ikon Allah haƙan sa ba zai taɓa cimma ruwa ba akan gurbatacciyar buƙatar sa. A lokacin da sinadarin allurar ya feso zuwa mahaifar wato cikin in da na ke babu irin jijjigar da ban sha ba, maganin ya so ya tarwatsa sassan jiki na wanda bai da ɗe da zama tsoka ba, da ikon Allah na koma bayan mahaifarta na yi wa kai na ɓuya duk da tsananin wahalar da na sha tsakanin rayuwa ko mutuwa, Allah ya zaɓa min rayuwa, tsahon watanni shidda ina bayan mahaifarta sannan na dawo na zauna daram a cikin mahaifarta na kuma ɗaura daga kwanakin da na tsaya,lokacin na san da cewa kainuwa dashen Allah ne, haka zalika zakaran da Allah ya nufa da cara ana muzuru ana shaho sai yayi abin sa. Tula_Kaltungo Yankin arewa maso gabashin Najeriya, Tula karamar hukumar kaltungo cikin jihar Gombe. Babban gida ne daga waje fentin da plaster da tsarin gidan ya tsaru ta yadda alkalamina ba zai iya rubuta adadin tsaruwar gidan ba. Cikin gidan ɓangare biyu ne mai kyau da kuma mara kyau. Sashin da za ka fa ra cin karo da shi, shi ne wanda ya ke hannun hagu kusa da ɗakin mai gadi, ɓangaren kamar ba a gidan yake ba. Sashin mu ginin blo ne wanda ba a karasa masa plaster ba, rufin ma babu ceilin, kofar ɗakin umma ƙasa ce cike taf yashi wanda yake shan shara a wajan Umma kullum kasancewar babu siminti ko interlock da akwai bishiyar bedi da tayi mana rumfa a kofar ɗakin.Umma ta na zaune saman tabarmar ta gaban ta wani babban baƙin baho ne wanda yake chike taf da goron tula sana'ar da ya karɓe ta hannu biyu kuma ta dogara da shi. Wani ɓangare na hannun dama a cikin gidan tsararran gini ne ginin blo mai kyau ya tsaru makurar tsaruwa, ƙasan barandar interlock ne aka kuma kewaye sashin da gajeruwar katanga mai huji huji, ma'ana an keɓance sashin ta yadda idan ba ka doshi wajan ba baka iya ganin cikin sashin da kyau....Muryoyin yara ne manya da kananu suke ta wasa, uku manya suna karatu, biyu yara masu shekaru goma suna ta wasa da keke kowa da nasa abin gwanin ban sha'awa. A wannan lokacin ina kwance saman tabarma gefen da Umma take zaune ina jan jiki wasa na na ke amma kunnuwa na suna ɗauko mun muryoyin yaran gidan daban daban izuwa kwakwalwata. Bana iya tashi tsaye balle nayi tafi...
App exclusive
Continue “FITILAR KWAI” in the app
The author limited this story to mobile. Open the app to read, listen, and keep your place.