FreeThe story
Synopsis
No synopsis yet.
Sample · 001
MATAR ZAYD…(free pages )page 0️⃣1️⃣Bismillahi Rahmanir raheemzayd yau bazaka kule ni a gidan nan ba Haba mana ka Hana kowa nawa zuwa gani na , ka hanani rike Babbar waya , kana neman ka haukata ni da hankali na , sanan Kai ka saka kafa ka fita yawon ka sai lokacin daka ga daman dawo wa zaka dawo cikin gidan nan wlh toh na gaji kazo mun wuya wani gigitacen marin da ZAYD ya sakar mata shine ya saka ta fara ganin dishi dishi, tayi tangal tangal zata fadi Allah dai ya taimake ta ta samu ta dafe bango ta tsaya, faisal ya nuna ta da yasta cike da gadara ya fara magana kamar haka“idan kin gaji da zama Dani ga hanya can malika ya nuna mata kofar fita daga falon , sanan yayi wani murmushin mugunta bazaki iya ba ko saboda idan kika koma wahala ce zaki sha , kalli gidan nan bakizo mun da komai ba ni nayi komai , kici mai kyau ki sha mai kyau ki saka mai kyau , lefe ma akwati nawa na kawo gidanku, sadaki nawa na bada gidanku, nawa na nake bawa iyayenki kafin su bani ke , nawa na kashe ma dangin ki , ke kanki bazaki iya Tuna nawa na kashe mki ba a haduwar mu zuwa auren mu aman duk bakya gani ko nine nazama marainin wayon ki har zaki kalle ni kice kin gaji da gidan nan okay ga hanya nan zaki iya komawa gidan uban naki I don’t have a problem with that ya fada yana sake nuna mata hanyar wajehawayen da take boyewa ne suka zubo ta kalleshi da jajayen idanuwanta, Girgiza Kai tayi alamun aa sanan ta juya dan komawa dakin ta tana kuka mai Çin raimurmushin gefen baki ZAYD yayi sanan ya furta “shashasha “ a hankula ya fice daga falonsaka key ya kulle ya kamar yadda ya saba..tana shigewa dakinta ta zube a katon gadon ta , tana fashe da kuka kamar kullum idan ZAYD ya shuka mata rashin mutuncitana cikin kukan ta ji kara a wayarta alamun shigowar text message , tana dubawa taga text message din faisal din Akan tayi hakuri abunda ya yi mata yanzu dai ta shirya yana nan zuwa kaita shoppingtashi tayi ta je gaban mirror tana goge hawayen dayake fita daga idanuwanta sanan ta kakalo murmushin dole ta ja numfashi tana kallon kanta a mirrorcikin murya kasa kasa tace komai ya wuce malika , ba ma komai bane ba ae daman ma aurata na samun irin wanan sabanin ki yafe masa kawai maybe an Chaja masa kai ne a office kuma kema kinzo kin tabo shi duk wanan maganganun da take ita kadai take magana da kanta Wanda ya Zame mata jiki ,tana gama fadin haka tayi hanyar wardrobe dinta ta bude ta dauki wata abaya mai kyau kyauta ce ZAYD ya bata ranar da ta fita unguwa ya kawo mata budurwarsa har kan gadon su na suna bayan tayi magana har suka samu sabani da buduwar , ZAYD bai ji kunyar wanke ta Mari ba a gaban budurwar, tana ji tana gani yarinyar ta hada inata inata suka saka Kai suka fice daga gidan suka barta tana ta faman kukaajiye buduwar tasa yayi sanan ya biya ta boutique ya siyo mata abayar ya ra...
App exclusive
Continue “Matar ZAYD” in the app
The author limited this story to mobile. Open the app to read, listen, and keep your place.