FreeArewaPen original
GONAR SHARRI...
- 1views
- 190chapters
- 0audios
- words
- 0likes
Share:
The story
Synopsis
No synopsis yet.
About the author
Marubuciya manazarciya.
Sample · BABI NA ƊAYA
GS 1.Tunda ta nufo cikin parlorn gabaki ɗaya hancinsa ya shaƙo masa lafiyayyun ƙamshin turarukanta masu matukar daɗi, gabaki ɗaya sai yaji tamkar bai shafa nashi turarukan ba saboda yadda nata ya yi bala'in yin tasiri a gabaki ɗaya wajan. Zaune Alhaji Sha'aban Sada yake akan 2seater hannunsa riƙe da wayarsa yana dannawa wanda shigowarta yasa shi ɗago kansa yana kare mata kallo mai cike da soyayya. Kyakkyawar mace ƴar gayu da kuma ƙwalisa da kallo ɗaya zaka yimata kasan don abun duniya ya tattara gareta, Murmushi suka sakarwa juna a lokacin da ta gama ƙarasowa inda yake yana ɗan matsawa can gefe alamar tazo kusa dashi ta zauna. Wani kallo tayi masa wanda yasa shi sakin ƙawataccen murmushi tare da maida kansa yana kallon side table ɗin da ya janyo zuwa gabansa wanda yake cike da tarin dukiya akai da alama amfani zai yi dasu. Zama Hajja Maimoon tayi tare da rungume shi tana kwantar da kanta...
Contents
Table of contents
Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.