FATTOMAHFree

ArewaPen original

RomanceFreeOngoing

FATTOMAH

  • 1views
  • 26chapters
  • 0audios
  • words
  • 0likes
Start reading

Share:

The story

Synopsis

ongoing

No synopsis yet.

Sample · Page 1&2

        *FATTOMAH*            MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION*Nanameera ce#**ALHAMDULILLAH!! ALHAMDULILLAH!! I'm so grateful to Allah subhanahu wata'ala for giving me the privilege to finished my book SHEIKH HEESHAM, I'm so grateful to my lovely fans I really luv you from the bottom of my heart nd my Role model Na'ima Sulaiman Sarauta(Nimcyluv) my regards to yhu Aunty nimcy. Now I'm back with another unconditional love book FATTOMAH don't miss it dears*Page 1-2.Hadari ne haɗaɗɗe a sararin samaniya banda guguwar iska babu abinda ake iya ji dubbannin mutane suna tattara kayansu domin kada ruwan saman ya iskesu domin a wannan lokaci ana tsaka da damuna ne babu tabbacin idan ruwan ya sauka ya dakata da wuri, cikin wannan yanayin take tafiya kamar wacce kwai ya fashewa a jiki, bakinta sai rawar sanyi yake da alama tana matuƙar jin sanyin da yake tashi. Yarinya ce ƙarama dan bazata shige 15-16yrs ba amma yanayin halittar jikinta zaka ɗauka takai irin 18yrs ɗin nan, tsayawa tayi da tafiyar ta durƙushe nan wajen tana riƙe ƙafarta sosai takejin ciwo a cikin ƙafar gashi kuma bata kusa zuwa gida ba babu kuɗi a hannunta bare tayi tunanin hawa ko keke napep ne dazai kaita gida, tana nan wajen durƙushe kusan 8mins wani mutum yazo shigewa har ya yi gaba sai kuma ya dawo ya tsaya yana kalllonta batareda ta san yana yiba"Keee me kike yi anan kina ganin hadari ya haɗo?"Sai a sannan ta ɗago runannun idanuwanta ta kalleshi amma ta gagara furta koda kalma ɗaya domin zuwa wannan lokacin jikinta banda rawa babu abinda yake wanda ke nuni da cewa ciwonta na gab da tashi, girgiza kai mutumin ya yi ya ce "ke kam kurma ce ko bebiya?" ba tare da ta ce komai ba ta miƙe tana dafe kanta wanda yake barazanar tsagewa a kowane lokaci. Gaba tayi mutumin ya bita da kallo yana mamakin hali irin nata to kodai bata ji ne???? ɗaga kafaɗarsa ya yi alamar bai dameshi ba sannan ya cigaba da tafiyarsa. Da sallama ta shige tsakar gidan nasu wanda bashi da girma ko kaɗan tana zuwa ta zauna gefen mahaifiyarta tana lumshe idanuwanta wanda take jin suna yi mata nauyi a kowane lokaci,"Fattum jikin ne?"Hawaye na gangarowa kan kuncinta ta ɗaga mata kai ajiyar zuciya ta sauke cikeda damuwa ta ce" sannu kinji Allah ya baki lafiya ya rabaki da wannan ciwon da yake damunki" shiru Fattomah ta yi ta kwanta kan cinyar mahaifiyarta nan da nan bacci ya ɗauketa. Zaune suke akan tabarma suna cin abinci cikeda kulawa ya ce" Faɗimatoh ya jikin naki?" tana kallonsa ta ce" Abbana da sauƙi kawai ƙafar ce har yanzu tana yi mini ciwo sosai" "Allah ya yaye miki gabaɗaya in Sha Allah" jinjina kanta tayi ta ce" Allah yasa Abba" ganin ba cin abincin take ba yasa ta ce" Fattum bafa kya cin abincin" turo baki gaba tayi cikeda shagw...

Continue reading free chapter

Contents

Table of contents

Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.

chapters26
premium16
11

21&22

Premium
Updated 2 years agoAvailable now
12

23&24

Premium
Updated 2 years agoAvailable now
13

25&26

Premium
Updated 2 years agoAvailable now
14

27&28

Premium
Updated 2 years agoAvailable now
15

29&30

Premium
Updated 2 years agoAvailable now
16

31-35

Premium
Updated 2 years agoAvailable now
17

36-39

Premium
Updated 2 years agoAvailable now
18

40

Premium
Updated 2 years agoAvailable now
19

BOOK 2 Page 41-45

Premium
Updated 6 months agoAvailable now
20

46&50

Premium
Updated 6 months agoAvailable now
21

51&55

Premium
Updated 6 months agoAvailable now
22

56&60

Premium
Updated 6 months agoAvailable now
23

61-65

Premium
Updated 2 years agoAvailable now
24

66&70

Premium
Updated 6 months agoAvailable now
25

71-80

Premium
Updated 6 months agoAvailable now
26

81-90 End

Premium
Updated 6 months agoAvailable now

Continue in the ArewaPen app

Unlock offline reading, audio mode, and sync your bookmarks instantly.

Download on the App StoreGet it on Google Play