FreeThe story
Synopsis
No synopsis yet.
Sample · Unrevealed Secret
🔪 MAKASHINKA 🔪( Ya na tare da kai )Storyand writtenByZeeyluv💞Author of.... FA'EEZAHand nowMAKASHINKA Ƙarƙashin jagorancin👇🏼 MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION ( M.W.A ) ***BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHIM Dukkan yabo da godiya ya tabbata ga ubangijin halittu, mai rahama mai jin kai, mamallakin ranar sakamako, gareka mu ke bautawa kuma gareka mu ke neman taimako, ka shiryar da mu hanya madaidaiciya, hanya wadanda ka yi ni'ima da rahama a garesu ba hanya wadanda ka yi fushi da su ba kuma batar da su. Ameen ya hayyu ya qayyum........Ya ubangijin sammai bakwai da kassai bakwai, Ya wanda ya halicce sammai da kassai a kwana shida, Ya ubangijin al'arshi mai girma, Ya ubangijin Musa da Harun, Ya wanda bai haifa ba kuma ba'a haifeshi ba, Ya wanda ba shi da abokin tarayya a cikin mulkinsa, Ya hayyu ya qayyum, Ya zuljalili wal ikram, Ya mallaisa ka mislihu shai'un wahu was-sami'un aleem, Ya ubangiji don alfarma masoyina, annaabina, annabi Muhammad (S. A. W) ka yi riko da hannayena a cikin wannan tafiya, ka ba ni ikon rubuta abun da zai zamo hujja agareni ba a kaina ba, ka bani ikon isar da sakon da na zo da shi ta hanyar da ya dace alfarma habibina annabi Muhammad tsira da amincin Allah su kara tabbata agareshi tare da iyalansa da sahabbansa baki daya...... INA MAI KARA MIKA GODIYA TA GA ALLAH DA YA SAKE BA NI IKON FARA SABON LITTAFINA MAI SUNA (MAKASHINKA ) INA FATAN ZA KU CIGABA DA NUNA MIN SOYAYYA TARE BANI HADIN KAI KAMAR YANDA KU KA NUNA MIN A LITTAFINA NA FA'EEZAH KOMA FIYE DA HAKAN..... NI CE TA HAR KULLUM ZAINAB BINT ABDULRAHMAN YAR MUTAN ZAZZAU(💋ZEEYLUV💞 ) LET'S GO💃💃💃01/12/1445AH ~ 07/06/2024<Repost>Book 1KAMAR DAI YANDA NAYI ALƘAWARI CEWA YAU ZAN CIGABA DA REPOSTING ƊIN MAKASHINKA TO GASHI NAN.......Episode 1Sanyin da garin ke ƙara ɗauka yayi daidai da ƙara cigaban ciwon mararta wanda tun kusan kwanaki uku kenan ta ke jinsa amma ganin yana hawa da sauka ne yasa ba ta mai da hankali kan ciwon ba tun da ta san time ɗin period ɗinta ne ya kusa. Abu kamar wasa sannu a hankali ciwon marar ya cigaba da karuwa tun tana iya dauriya har ciwon ya fara cin karfinta. Shigowar Ammi ɗakinta Ammi ta yi nan tarar da ita kwance a ƙasa tama bar kan gadon na ta baki ɗaya sai murƙususu ta ke yi a ƙasa. Wani irin murɗawa da mararta ya sake yi tamƙar hanjin cikinta za su fito waje hakan ya sa ta furta "Inalillahi wa'inna ilahirraji'un! Wayyo Ammina zan mutu!" Da hanzari Ammin ta isa gareta tana faɗin "Subahanallahi Ma'eesha marar ne"? "Gaskiya ya kamata muje asibiti don ni banganewa wannan ciwon marar haka da yaƙi ci yaƙi ƙarewa, wannan ko naƙuda dai iyakacin wahalar ke...
App exclusive
Continue “MAKASHINKA” in the app
The author limited this story to mobile. Open the app to read, listen, and keep your place.