FreeArewaPen original
Karen Bana
- 1views
- 5chapters
- 0audios
- words
- 0likes
Share:
The story
Synopsis
No synopsis yet.
Sample 路 Chapter 1
馃挒 *KAREN BANA*馃挒( Cigaban laifin mijina )*1*BY *Reefat yahya*Marubuciyar*Nida shugaban kasa**Shine zabina**Mai sona**Rayuwar yau**Hukuncin uwa**Mace zinariya**Hijra**Jauro bajam**Nasarar Rayuwata**Laifin mijina ne**SIHIRTACCIYA*N now...*Karen bana*Bismillahir rahmanir Raheem da sunan Allah Mai rahama Mai Jin Kai Allah yasa mukaru da abinda ke ciki Allah yasa a gama lafiya amin, nagode masoyana Ina Mika sakon godiyata da Kuma gaisuwa a gareku a duk inda kuke a fadin duniya馃檹馃徎馃檹馃徎馃グ *Zaki biam , ukum local government Benue state* unguwar Hausa quarters unguwa ce cikin garin Zaki biam dake karamar hukumar ukum dake cikin jahar Makurdi Wato Benue state dake arewacin Nigeria, akwai kabilu da dama cikin wannan gari amma yawancin kabilar Tiv sukafi yawa akwai hausawa da Kuma idoma da sauransu. Malam Sule direba Yana d'aya daga cikin mazauna wannan unguwa ta Hausa quarters ya kasance kabilar Tiv ne sana'arsa shine direba Wato Yana tuka motar bus daga Benue zuwa wasu jahohi a fadin kasar , cikin tafiye tafiyen nasa ne Allah ya hadashi da matarsa ta biyu Aishat bafulatanar yola a yayinda matarsa ta farko ta kasance kabilar tasu Wato Tiv sunanta Hari , shekararsu biyar da aure Allah Bai Basu haihuwa ba wannan dalilin yasa malam sule Neman aure har yayi dace ya sace zuciyar Nana Aisha wacce sai da aka Sha fama kafin iyayenta suka amince da zancen auren nasu saboda banbancin yare. Hari irin matan nan ne Masu zafin kishi gata guntuwa ga masifa ga kishin tsiya ga baki da yawan surutu yayinda Nana Aisha ta kasance shiru shiru ga kawaici da alkunya , wannan sanyin nata ne yasa take Shan wahala a hannun Hari . Bayan auren nasu da wata biyar Allah ya azurta Nana da samun juna biyu , Hari na ganin haka hankalinta ya tashi ta kasa zama sai shiga da fita take tana Neman mafita masifa da tashin hankali kuwa na safe daban na yamma daban haka Nana Aisha ke shanyewa tana kokarin boye damuwar , malam sule Yana noman doya shiyasa yake da rufin asiri domin ya rike sana'a biyu . Duk da cewa baya zama sosai amma Yana kokarin farantawa iyalinsa idan ya dawo Yana Siyo musu kayan more rayuwa dai dai gwargwado Kuma Yana iya bakin kokarinsa don ganin ya kwatanta adalci tsakaninsu , a haka har cikin Nana ya shiga wata tara daga wannan lokacin ta kasance cikin jinya yau lafiya gobe babu wannan dalilin yasa sule ya rage yawan tafiye tafiyen da yake Yana tare da Nana Aisha Yana Bata kulawa nan kuwa Wani sabon tashin hankali ya taso inda Hari ta fara jefa maganganu iri iri har sai da malam sule ya taka mata birki ta hanyar nuna mata cewa idan ta sake tada fitina ta wuce gidansu donhaka ta ja bakinta tayi shiru, ranar wata litinin ranar da Bazasu manta ba a wannan ranar Nana Aisha ta haifi santaleliyar y'ar ta mace kyakkyawa Mai kama da ita sak! Cikin kankanin lokaci A...
Contents
Table of contents
Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.