FreeArewaPen original
Ƙwai A Baka
- 1views
- 2chapters
- 0audios
- words
- 0likes
Share:
The story
Synopsis
No synopsis yet.
About the author
الحمد الله While others talk, I write… turning feelings into words and silence into stories 🖤 because my pen never lies ✍️ and my mind is full of stories waiting for the right moment to be told 🔥
Sample · Thriller
Murɗawar da cikina yake yi ne ya sa ni miƙewa daga kwancen da nake ina dafe cikin, wata irin kartawa yake kamar za'a cire ƴaƴan hanjina, amai na ji na fara ji da sauri na tashi na fita waje, a tunanina ba komai ne ya janyo mini abin da nake ji ba face yunwa, dan kusan kwana biyu kenan, ba mu ɗora tukunya ba sai dai a sayo kunun tsamiya, idan ya samu idan bai samu ba haka zamu kwana da yunwa, ga ƴaƴan nawa duk yara ne babu wanda ya haura shekaru sha biyu.Amai na dinga yi ba ƙaƙƙautawa, wani irin jiri nake ji da zazzaɓi, jikina sai karkarwa yake kamar 'yar bori , ji nake kamar zan faɗi ƙasa, da ƙyar na lallaɓa na koma ɗaki.Har zan wuce ta gaban madubi na tsaya na kalli kaina, Rasss! na ji gaba na ya faɗi ganin na ɗashe na yi fari ga wata uwar rama da na yi. Nafi kwana biyu ban kalli madubi ba, "Kar dai ciki na kara samu?" Na tambayi kaina wata zuciyar ce ta bani amsa da "Eh ki kalli yanayin ki mana irin na masu ciki" ɗayar zuciyar tace "A'a kawai rayuwar da kuke ciki ce ya sa ki zama haka", "Hasbunallahu wa-niimal wakil, ina zan kai wannan cikin ni Halima" shiru na yi cikin zullumi, kasancewar shayarwa nake yi, ba na al'ada, dan haka ba zan tantance ba.Wani tunani ne ya zo mini a rai da sauri na koma waje na nemi abu na zuba gishiri, banɗaki na je nayi fitsari na haɗa su guri ɗaya ina jiran ganin sakamakon, bai fi daƙiƙa biyar ba ya koma ruwan madara "Innalillahi Wainnaillaihir-rajiun" shine kawai abinda na faɗa dan ta tabbata ina da ciki.Tamkar na gano tafiya lahirata haka hankalina ya tashi, cikin tsananin zullumi da tashin hankali!********Ɗagowa yayi ya kalleni yana watso min idanunsa sannan yace "Na gaji da zama dake ne AMATUL-ISLAM""ABAAN" na faɗa da ƙarfi ko kallona beyi ba balle ya ce min wani abu, wani kulutu ne ya tsaya min a zuciya na daure na cigaba da cewa "Tunda na dawo gidan nan ka daina kwana a ɗakina ko nazo gurinka sai ka dawo falo, kyautatawar da kake min da duk ka watsar, kuma bayan kasan a asibiti haka suka ce ka ringa kyautata min ko zan samu sauƙin ciwon nan""Da yoyon fitsarin zan kyautata miki? Duk kin ruɓe nawa kike AMATUL-ISLAM da zaki kamu da wannan ciwon?" Ya faɗa minDumm zuciyata ta buga dai-dai da wata irin tsawa tare da saukowar ruwan sama daya sauka a gari, ban san lokacin da na faɗa kan kujerar dake kusa dani ba, na hau cewa "Hasbunallahu wa ni'mal wakeel saboda haihuwar dana yi na kamu da lalurar nan amma zaka min gori?, Gurin haihuwar ɗanka na samu wannan matsalar fa Abaan kayi min adalci yanzu?"na ƙarasa faɗa zazzafan hawaye na zuba a idona"Ohhhh yanzu na gane inda kika dosa ai ba dole nayi miki kika aure ni ba"shima ya ce min, shiru ban ce masa komai ba, sai can naji ya ce "Ke ni tsaya kiji na gaji da zama dake wallahi, Kije na sakeki saki Uku"A hargistsena ɗago kyakkyawan fararen idanuna ina kallonsa tare da ce...
Contents
Table of contents
Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.