FreeThe story
Synopsis
No synopsis yet.
About the author
Anatomist, Lab technician, beauty vlogger( make up artist, fassion designer), bussiness holder ( shadda, baby wares), and a novel writer.
Sample · 1
Tana tafiya murmushi na kuɓuce mata, ba ta san sanda yake zuwar mata ba. Ita kanta idan aka ritsa ta aka ce ta faɗi murmushin me take yi ma, ba ta san me za ta ce ba. Illa iyaka tace tana jin wani farin ciki na ratsa mata ƙirji. A haka ta cigaba da tafiya har ta isa kan kwanar da za ta sha ta isa layinsu, babu zato babu tsammani se ga Sadiq a gabanta."Ranki ya daɗe irin wannan sauri haka, ina ta bin ki, kina daɗa yi mini nisa. Kin ga mantuwa kikayi, zuciyata taji baza ta iya haƙura ba, se ta kaiwa wannan zinariya abinda yake nata kuma mallakinta." Ya miƙa mata takardun hannunsa dake cikin envelope fuskarsa ƙayace da murmushi mai daɗin kallo.Wani sanyi na ratsa zuciyar ta, take kallonsa har ya kammala magana, wushiryar dake bakinsa, ns ƙara kyawun zancen sa, ga sajen da ke gefen fuskarsa, se ƙallin baƙi suke yi, gaba ɗaya kyawun sa ya maƙale a idaniyan ta. Da ƙyar ta sami courage ta buɗa ...
Contents
Table of contents
Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.