FreeArewaPen original
'YAN TIRIRRISHI! (Zombies Story)
- 1views
- 6chapters
- 0audios
- words
- 0likes
Share:
The story
Synopsis
No synopsis yet.
About the author
Nainarh KD – Nkd's “Every heart has a story — I only give it words.” 📞 Phone Number: *** or ***
Sample · 1&2
♡💃YAN TIRIRRISHI 🐓💫 (_~Ajalin Kaza!!!~_)"When fate calls, will you answer?" Story And Written By;Khadeejarth Sabi'u Yahyah Nainarh KD, As you know me. The Writer of;1. SARAUNIYAR KYAU 2. ANEESERH (THE INNOCENT GIRL)3. TSANTSAR SO 4. KIN CUCENI 5. RANAR BIYAN BUƘATA 6. BA TABBAS 7. CAPTAIN AYUSHERH 8. UMMULJAANNAH 9. ‘YAN TIRIRRISHI!*** new blockbuster novel from the Nainarh KD the perfect pen, the story with the full of;.# Love # Horror # Zombie's # Comedy # Against The Perfect Exceptional Love!!💯💞💘Dedicated to Maman Afrah..(Allah ya biya miki buƙatun ki na Alkhairi My ta musamman.🙏🤩Copy is not allowed.¡!Ba kuma zan Lamunci a canzan labari kota wata siga ba.¡!Perfectly Pen's 🖊️ بسم الله الرحمن الرحيم...1&2Ragwajab kakeji lokacin da Motar ta tsaya cak ta bada wannan sauti. A hankali ƴan matan suka fara saukowa daga Motar suna ya mutsa fuska kowacce da abin da ya dameta aƙalla za su kai su goma sha ɗaya.Cikin ƙosawa Rabi'ah ta ce. “wai driver mun ƙari so garin ne da naga an tsaya ko ya ya?”Ta ƙare maganar lokacin da ita ma ta sakko daga motar tana miƙa na gajiya, bata jira driver ya bata amsa ba ta kalla Haleema dake jingine da motar tana faman latsa waya ta ce. “Haleema wai me ke faruwa ne ya naga an sauke mu anan kuma ban ga alamun gidaje ba sai bishiyoyi....”“karki damu ai mun kusa ƙari sawa, Suhaima ce ta nemi a tsaya wai fitsari takeji.”Cewar Budurwar da Rabi'ah ta kira da Haleema tana yi ma ta nuni da wurin da Suhaima tabi.Shiru Rabi'ah ta yi jin wacce a ka ambata, sai ta taɓe baki tare da jingina da motar tana ɗan kallon dajin har idonta ya sauka a kan ta, dariya ta ɗan yi sannan a fili ta ce.“wai ke, ko dai dole kika ma waccan Yarinyarne a kan sai ta biyo mu?”Ta faɗa tana taɓo Haleema tare da yi ma ta nuni da Wurin da Budurwar ta ware take zaune a takure sai lokacin Haleema ta lura ta ita dan a tunaninta bata fito daga Motar ba ma, girgiza kai Haleema ta yi. “bana son sa ido fa Rabi'ah yanzu mene ne ruwanki da ita?”Rabi'ah tana ƴar dariya ta ce. “babu fa amma gani nayi sai kace wacce a ka yi ma dole a kan sai ta biyo mu...”“ke dai kika sani.”Cewar Haleema tana ci gaba da ƙoƙarin kiran lambar da take yi tun ɗazu sai dai saboda yanayin wurin da suke babu network ya sa kiran bata shiga.Rabi'ah kuwa nutsuwa ta yi tana ƙirga yawan ƴan matan dariya n...
App exclusive
Continue “'YAN TIRIRRISHI! (Zombies Story)” in the app
The author limited this story to mobile. Open the app to read, listen, and keep your place.