FreeArewaPen original
BA'ABORAN NAMIJI
- 1views
- 5chapters
- 0audios
- words
- 0likes
Share:
The story
Synopsis
No synopsis yet.
Sample · 1&2
*BA'ABORAN NAMIJI*NA*BINTA UMAR ABBALE* *Shimfi'da*1&2"Kulsumu! kina ina? Fito nan, Wallahi yau a gaban kowa za'a yi ta ta k'are na gaji da wannan halin na ki".Zuciyata ta harba tare da zullumin yau kuma mai aka shiryo mini ni Ummu Kulsum?"Na fita ina hirji.Gabadaya matan gidan suna tsaye sun yi cirko cirko tamkar zakaru.Ya kausasa murya ya ce "Kulsum wa na d'amkawa ragamar kulawa da store din abinci?" Murya babu amo na ce ni ce Amma me ya fa.....Ya daga hannu a zafafe ya ce "full stop diga aya kawai.Ta ya ya za'a ce mini babu man gyada da indomie a gidan nan?"Zuciyata ta buga da tsananin gaske. Domin ni kaina na ka'du da furucinsa. Idan lissafina daidai ne. To Kuwa yau kwanaki goma kacal da bude jarkar mai 25 Lita. Taliyar yara kuwa yau kwanaki uku da ya shigo da katon biyu. Sau daya kacal na dafa domin kuwa su ban ga sun dafa ba ma. Amma ace yau babu. Lallai dole ya yi fad'a ban ga laifinsa ba a yanda rayuwar nan ta yi tsanani.A sanyaye na ce "Allah ya huci zuciyarka Yaya amma wallahi ban san komai ba akan wannan sha'anin. Kuma Dole idan iyalai suka yi yawa sai an yi hak'uri saboda hidima tana k'aruwa za'a gyara In sha Allah"Ya ja tsaki ya ce "Kina nufin dole na yi hakuri na zuba ido kina neman yi mini sanadin shiga ba'kin talauci?Nawa ake siyar da kwalbar mai ne bare jarka? Wato bak'in cikin da ake cewa kina yi ne yake neman fitowa muraran ko?"Nan da nan zuciyata ta karye hawaye ya cika idona murya na rawa na ce "Yaya da bakinka kake jifana da yi maka bak'in ciki a cikin gidanka?"Maimakon ya sassauta sai kuwa ya sake fusata ya ce "Ba iya bakina kad'ai nake magana ba, har da zuciyata. Domin mugunta da bak'in ciki ya sanya kike kwashe mini kayan abinci".Kuka ya ke ce mini. Na kasa cewa uffan domin zuciyata ta yi nauyi ainun! To na kwashe kayan abinci na kai su ina?Ya ja tsaki ya ce "Kukan ki ya k'are Kulsumu Je ki dauko mini mukullin store din hannun ki. Na yi iyakacin kokarina akan na baki girmanki amma abin ya faskara dan haka idan girkinki ya zo sai ki karba a hannun Nadiya."Kafin na yi magana. Nafisa ta yi fit ta ce "Ai kuwa idan kana nufin ita zaka bawa mukullin sai dai a raba girki amma tabbas ban yarda da alwalarta ba bare ta ja mu jam'i."Aliya da ita ce amarya ta ce "Ai kuwa dai nima ban yarda ba.Kukana ya tsaya cak. A dalilin na fahimci dukkansu sun had'a kai ne dan su kai ni k'asa.Amma kuma da za'a shugabantar da wata a cikinsu ba ni ba, to zasu koma rikici da junansu.Na yi k'asa da kaina.Ina jin sauki da jarumta na ratsa ni. Wato duk da ni kad'aice ban haihu ba a gidan ba ni da ko kaza amma na dame su, na yi musu karantsaye a zukatansu.Duk wacce ta kwaso makircinta a kaina zata sauke shi. Abin da yake d'aure mini kai shine; ba ga ni suka yi yana fifita ni ko yana tausaya mini ba. Asalima wani cin...
Contents
Table of contents
Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.