FreeThe story
Synopsis
No synopsis yet.
About the author
Am a writer,i dream while awake.
Sample · DUNIYA TA! DUNIYA TA!!
*D U N I Y A T A*🌎🌍🌏*_HUGUMA_**_DANDANO DAGA CIKIN FITATTUN LITATTAFAN ZAFAFA BIYAR_**_a DUNIYATA! Bansan komai ba sai MARAICI K'UNCI baqinciki da tsanani hadi da manya manyan qalubale_**_DUNIYATA ba irin duniyar sauran bace_**_DUNIYATA tasha banban da duniyar sauran bil'adama dake rayuwa_**_wata irin juyayyar duniya ce da idanuwanta suke kallon rayuwa da mabanbanciyar FUSKA_*Waye ya turota?,maqarqashiya ce ko kuma hadin baki?. Sake Waiwayowa tayi gareshi karo na biyu. Kallon da tayi masa ta fahimci yakai matakin qarshe a iya haqurinsa"Malam naseer......ka shirya biyan duka bill na siyayyar sabreen ko kuwa tunda kai ka kawo qafafunka duk da gargadinka da tayi?""Sabreen?" Ya maimaita sunan yana kallon idanunta. Kiran sunan sabreen da tayi a maimakon basma shi ya batar masa da tunani cikin taqi qanqani."Zai biya duka bill din.....na gode sosai" Ta fadiwa ma'aikacin"Naga uban wanda zai sakani biyan kudin nan......na fahimci na sakar miki fa da yawa" Ya furta da zafi sannan a zafafe ya biyo bayanta. Ya tsammaci zata nemi guduwa ko ta gudu dinma,amma ga tarin mamakinsa tun bai qarasa isowa gareta ba taja cak ta tsaya tana sauraron isowarsa."Ka samu aminci game da haramtattun kayanka da aka aiko maka dasu ta cikin jirgin ruwan dake tsakanin River Benue da riba niger?.......ko kuma ka shirya aci kasuwar wannan sirrin da jami'an tsaron dake neman kayan tamkar yadda mutuwa ke neman ruhi?". Kamar wanda aka sanyawa sasari akan tsaida haka yaja wani wawan burki. Kallonta yakeyi da madaukakin mamaki. Wanne irin hadari ne da ita har haka?. Wanne nisan ji da gani ne da ita?,nisan binciken da ya bata damar gano birnannen sirrinsa da ko matarsa da suke kwana daki daya su tashi daki daya bata sani ba?."Ka biyasu kudin siyayyarsu duk yadda suka buqata,na barka lafiya Alhaji Naseer" Ta qarashe maganar tana takawa hankali kwance tana fita kwata kwata daga wajen."Malam qaraso ka bada kudin......ta atm ne ko cash zaka bada?" Muryar ma'aikacin ta katseshi daga bin burbushin hanyar data wuce da kallo ya juyo zuwa wajen biyan kudin yana sauke wani irin gauron numfashi me nauyi da zafi cikin tsananin mamaki da tsoro.*_AKWAI RUFAFFEN SIRRI ME WUYAR FAHIMTA_**_AKWAI QALUBALE_**_BAHAGUWAR FAHIMTA_**_RAUNIN ZUCIYA_**_TAKUN SAK'A ME ZAFI_**_ZAZZAFAR SOYAYYA ME SHAMMATAR ZUKATAN DA SUKAYI NISA DA TUNANIN DACEWAR WANZUWARSU QARQASHIN INUWA GUDA_
App exclusive
Continue “DUNIYA TA🌏” in the app
The author limited this story to mobile. Open the app to read, listen, and keep your place.