FreeThe story
Synopsis
No synopsis yet.
Sample · Episode 1
*GAWA TAFE* (Zombies story) On2025 *©Zahra Royal Star*Episode 1 *General hospital Katsina State Nigeria*"Innallihi wa'inna alaihir raju'on, Farida waye ya take ki da mota har hannunki ya k'arya haka?" Kuka Farida kawai keyi mai cike da tsananin rad'ad'in zuci da azabar da hannunta ke mata.Kwance take akan gadon marassa lafiya, irin na asibitin. Hannunta ta kalla ganin yadda ya kunbura har yayi fushi da waya, wani miyau mai zafi ta had'e a mak'oshinta tana kallon abokiyar zaman Mahaifiyarta wacce duk ita ce silar shigarta cikin wannan wahalar, domin da baccin bata d'ora mata tallar da bata so ba, da duk hakan bata faru ba."Inna Zubaida wani ne a mota ya bige ni, kuma bai tsaya ba, yayi tafiyarsa, sai wasu Mutane k'alilan ne suka kawo ni asibitin nan""Dalla can rufe min baki, ai ni wallahi ni ce kika jama asara, yanzu ubanwa zaije wajan aikin ki? Kin kuma san inda k...
Contents
Table of contents
Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.