BANAFSHA BOOK 1Free

ArewaPen original

MysteryFreeCompleted

BANAFSHA BOOK 1

  • 1views
  • 36chapters
  • 0audios
  • words
  • 0likes
Start reading

Share:

The story

Synopsis

completed

No synopsis yet.

About the author

Alkalamina ƴanci na ne, ina roƙon Allah kar ya bani ikon rubuta abun da ba zai amfani al'umma ba, ina amfani da baiwa ta na rubutu ne, wurin amfana da al'umma gami da nishaɗantar da su. Ku cigaba da biyo alƙalamina domin samun ƙaruwa, saban ilimi da kuma nishaɗi duk a lokaci ɗa...

More from @lelelady18

Sample · Page 1

A heart touching story, mai dauke da soyayya, yaudara, da kuma cin amana, duk a cikin littafin Banafsha,Duk mai bukata yayi following link din domin samun littafin *** Miss 'LL (lele lady)Da sunan Allah mai Rahama mai jin Kai ya Allah kamar yanda na fara wannan littafin lfy ya Allah ka bani ikon kammala shi lfy.PAGE 1Yanayin ne na damuna domin kuwa hadarin daya mamaye dajinneya nuna hakan dajin yayi duhu sosai saboda hadarin daya haduGudu takeyi cikin fitar hayyaci tana gudu tana mai waiwayon bayanta, sosai take gudun tana fitar da haki, gudu takeyi na ceton rai hannun ta rukeda jinjiri nade cikin kakkyawan farin towel da alama jinjirin dake hannun ta ya suma koma ace babu rai a jikin shi duba da irin yadda take gudu tana jijjiga shi ba tare daya ko motsa baAddu'a take yi akan Allah ya kawo musu dauki domin bata jin zata iya bari rayuwar wannnan jinjirar ya salwanta domin kuwa ita kadai ce zata zama mukullin bude war wani sirri, ita ce zata zama silar tonuwarwani babban kullin da yayi silar rugujewar rayuwar mahaifanta dama mutane da dama, Amma ta yaya?Domin kuwa bata tunanin wayannan miyagun mutanen da suka biyosu zasu bar koda gawar suce a gani ballanta na har su tsira da ransu Amma duk da haka bata cire dai da hukuncin ubangiji ba domin kuwa shine mai kashe wa kuma shine mai rayawa.Gudu ta cigaba dayi tana mai cigaba da karanto duk addu'o'in da suka zo bakinka, bata jinzata iya bari rayuwar wannan jinjirar ta salwanta koda hakan yana nufin ita zata rasa nata ranne, cikin fitar hayyaci ta cigaba gudu jefa kafarta kawai takeyi ba tare da ta san inda take sata ba, cikin rashin sa'a tayi tuntubeda wani ice nan take tayi kasa zata kife da sauri ta kara tallabe jinjirar dake hannun ta domin kada ta bugu ko kuma wani abun ya sameta cikin rashin sa'a ta fadi akan wani dutse hannunta ne ya bugu akan dutsen,wani marayan ihun azaba ta saki domin kuwa ba karamin buguwa hannunta yayi ba, hawayen dake zuba kan kuncinta ne suka kara kaimi wurin zuba nan take hannun nata ya fara nuna alamun kunburi da alama targade ta samu ko karaya,alamun gudun wayanda suka biyota ta ne ta faraji, nan take taji wani karfi ya zomata, cikinazama ta yunkura ta mike duk da azaban radadin da hannun ta ke mata hakan bai hanata cigaba da gudun ba domin kuwa tanajin dole ne ta ceci rayuwar wannan dake atareda ita, gudun taci gaba dayi wasu zafafan hawayen cigaba da sintiri akan kuncinta,Cikin sa'a ta hango wani karamin kogo adaidai lokacin wata iska ta taso alamun hadarin daya hadu yana dab da zubda ruwa, kara karfin gudun ta tayi tare da nufan wannnan kogon data hango duk da yadda iskan ke shigan mata ido amma hakan bai hanata gudun ba sai ma kara kaimi da tayi, dan tana tunanin ta samu hanyar da zata ceci jinjiran,tana karas...

Continue reading free chapter

App exclusive

Continue “BANAFSHA BOOK 1” in the app

The author limited this story to mobile. Open the app to read, listen, and keep your place.

Download on the App StoreGet it on Google Play