FreeArewaPen original
MATAR HABIBI
- 1views
- 45chapters
- 0audios
- words
- 0likes
Share:
The story
Synopsis
No synopsis yet.
About the author
#Muslima #LubnaSufyan #Daughter #Wife #Mother #Writer #ArchitectInTheMaking #Pa #Tea #Naruto #Glasses #Hijabee Facebook: Lubna Sufyan Instagram: LubnaSufyan ***: *** Idan har ka taba k'aruwa da littafina ta kowacce siga, ka tayani rokon Allah da ya yafe...
Sample · 1
Daya tashi zaune, saurarawa yayi, wai ko kunnuwanshi ne suke son yaudararshi, da gaske sallame sallah ne yakeji"Inalillahi wa ina ilaihi raji'un..."Ya furta yana janyo wayarshi, ya duba lokaci, karfe biyar da minti goma sha biyu, cikinshi yayi karar daya tabbata ta yunwa ce tunda daren jiya ba wani abincin kirki yaci ba, sai kuma cikin nashi ya sakeyin wani sauti, wannan karin na tashin hankali ne, ya kuwa diro daga kan gado cikin hanzari yana bude kofar dakin shi ya nufi hanyar da zata sadashi da dakin Jamila, ko tunanin ya zurfafa ba zai iya tuno ranar da Jamila ta makara ba, in ba don ita ba ai da ya tabbata makota sun sakashi a jerin mazan da ba'a gani a masallaci sallar asuba"Jamilaa..."Ya kira bayan ya tura kofar dakin nata, a kwance ya ganta kan darduma, jikinta sanye da hijabi ruwan toka, ta dunkule jikinta waje daya, alamar da tayi sallah bacci ya dauketa a wajen, karasawa yayi ...
Contents
Table of contents
Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.