FreeThe story
Synopsis
No synopsis yet.
Sample · Babi na ɗaya
When we first met, I smiled because I knew you were going to be important to me someday.Maryam tana zaune a kan kujerarta, a ɗakinta mai tsari da kyau. Kamar yadda ta saba, komai na ɗakin yana cikin tsafta— launin pink da white sun ƙawata bangon, sai ƙamshin turaren vanilla da ke ta yawo a iska.Tana a zaune da littafin Economics a hannunta, idanunta sun nitse a kan shafukan, tana kokarin fahimtar wani concept mai wahala. Amma kafin ta iya zurfafa tunaninta, ta ji muryar mahaifiyarta daga waje."Maryam! Maryam!"Ta ajiye littafin a kan study table ɗinta, ta miƙe. "Na'am, Mummy," ta amsa, ta fita zuwa babban parlorn gidan.Hajiya Binta na zaune a kan kujerar falo, hannunta riƙe da waya, amma idanunta a kan Maryam. Da alama akwai wata muhimmiyar magana da take so ta faɗa."Mummy, gani," Maryam ta faɗa tana zama a gefanta, tana kallon fuskar mahaifiyarta da ke cike da murmushi."Yauwa Mamana, dama ina so na sanar da ke cewa na samo miki aiki a GT Bank, inda Uncle Yusuf naki yake aiki."Hannuwan Maryam suka saki a kan cinyoyinta. "Oh Allah, Alhamdulillah! Mummy, da gaske?" Ta faɗa cikin muryar farin ciki, idanunta cike da mamaki. Kafin Hajiya Binta ta kai ga amsawa, ta ruga ta rungume ta sosai, numfashinta yana sauka da sauri saboda farin ciki. "Nagode sosai, Mummy! Allah ya saka da alheri. I am very grateful.""Yauwa uwata!" Hajiya Binta ta shafa kanta, ta yi murmushi. "Hakika kina da kwarewa, dole ne a yaba ki. Yanzu ranar Monday za ki fara aiki. Kuma zan tura miki 500K a account ɗinki, ki je ki sayi kayan office, jaka, makeup, da duk wani abu da kike buƙata."Maryam ta sake jin wani sabon nishadi ya ratsata. Ta riƙe hannun mahaifiyarta sosai, tana jin daɗin wannan soyayya da kulawa."Okay, Mummy, I will do so. I can't believe I have finally gotten a job, da nake so, kuma aiki a GT Bank, inda Abba ya yi aiki. Allah ya jikan Abba na."Hajiya Binta ta lumshe ido, zuciyarta ta ji sanyi. "Amin, Allah ya jikan mijina."***Ranar Farko a GT BankRanar Litinin, Maryam ta iso GT Bank da motarta. Ta saka kayan riga da wando na office wear masu kyau, amma ba su da hayaniyar launi. Mayafinta ya zagaye fuskarta yadda ya kamata, kuma ba ta yi makeup ba, amma hakan bai hana hasken kyanta bayyana ba.Ta sauke ajiyar zuciya a yayin da ta shiga cikin bankin, hannunta riƙe da folder ɗin papers. Idanunta na yawon duban cikin bankin, tana kallon yanayin wurin, , sai taji an kira sunanta:"Mairo!"Tayi saurin juyowa. Idanunta suka sauka a kan Uncle Yusuf_ƙanin mahaifinta wanda yake ji da ita, yana tsaye da murmushi a fuskarsa. Cikin hanzari ta nufi gare shi, ta durƙusa kaɗan tana gaishe shi."Ina wuni, Uncle.""Lafiya kalau, Mairo. Na ji daɗi kin zo da wuri, ba ki yi late ba. This is good."Murmushi ya bayyana a fuskarta. "Thank you for your compliment, Uncle.""Bari in nuna miki office ɗ...
Contents
Table of contents
Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.