RAI DAI...Free

ArewaPen original

AdventureFreeOngoing

RAI DAI...

  • 1views
  • 33chapters
  • 0audios
  • words
  • 0likes
Start reading

Share:

The story

Synopsis

ongoing

No synopsis yet.

Sample · 01

*Haƙiƙa ƙaddara mahaɗi ce ga kowace rayuwa,yayinda haƙuri kan tallafawa duk wani mai fuskantar jarabawa...kunyi haƙuri?. Kokuwa dai kun zub da makamakan kun zama ƴan kallo....*★ Baki ɗayansu miƙewa sukai suna zuba min ido ganin yanda na nuna ko ajikina bayan kuma ni kaina nasan nayi kuskure ba ƙaramiba.... Gwaggo ce ta fito daga ɗakin ta tana faman gyara zaninta data soke tana cewa."To yanzu ku da kukai cirko-cirko zaku iya hana masu gida yin hukunci ne...ai tunda ita batasan yanda akecin arziƙiba saiku barta taci ubanta a hannun Magaji idan ya dawo dan nasan bazai taɓa raga mata kona misƙala ba".Tana kaiwa nan ta ɗauki buta ta nufi wajen wanke-wanke dan hannu zata wanke dama..Kallona Maama tayi zatai magana Yaya tai saurin ɗaga mata hannu tareda kamo hannuna muka shige ɗakin mu dake jikin ɗakin Gwaggo...wani wawan ranƙwashi Yaya ta kaimin nai azamar duƙawa ina rumtse idona tsam..."Kinganki ki kiyayeni da wannan ƴar banzar ƙiriniyar taki"Dariya nai ina kaiwa zaune dab da ƙafafun Maama data shigo yanzu ta zauna akan carpet ɗin dake shimfiɗe a ɗakin namu. Kallon Maama nai yanda ta zauna tai shiru kamar ba ita agun,sam bana ƙaunar ganin mahaifiyata acikin damuwa saidai na rasa me zanyi a duniyar nan na sanyata farin ciki da walwala kamar kowacce uwa....Mukan jima kafin wata hira ta haɗani da mahaifiyata wato Maama daga uhmm sai um'um,sam babu wata hira ko wata tattaunawa irinta ƴa da uwa da ake har a fahimci juna. Idan kaji bakin Maama to tare suke itada Yaya saika rantse ba itake ɗinke bakintaba idan nazo waje,abin yana matuƙar damuna sosai saidai akoda yaushe Yaya wato kaka ta mahaifiyar Mama takan yimin nasiha akan na dinga yiwa mahaifiyata addu'a komai zai wuce.....sosai muke hira nida Yaya kamar itace ta haifeni haka take jana ajiki taji matsalata ta bani shawara idan nayi ba dai-dai ba tayi min faɗa inta kama zane ni, ga shagwaɓa ni da take duk ni kaɗai.Yanzu ma hira muka sha sosai bayan Yaya ta gamai min nasiha gameda rashin kunyar danaiwa Aunty Jameela,Maama tana gefe a zaune tana faman rubuce rubucenta a juter....ba mune muka tashiba sai da aka kira magrib sannan kowa ya miƙe ya fito danyin alwala.★Ina zaune ina duba littafan makaranta ta Gwaggo ta fito daga ɗakin ta dan duk nida Yaya da Mama muna tsakar gida a zaune hasken solar ya haske ko ina agidan masha Allah."Ke Jannah wai bazakije ki amso abincin dare bane ko kuwa sai yunwa ta kasheni kin huta....ko gyatumarki kike so na aika ne"?.Tsaf na ɗinke fuskata ina rufe littafin dan banda ganin idon Yaya da Maama ba abinda zai hanani yaɓawa matar nan magana,saidai kuma ni kaina nasan rashin kyautuwar yin hakan kuma Yaya zataga kamar ban ɗauki nasihar da tai min ba... miƙewa nai na ɗauko takalmina dake can ƙofar ɗakinmu na sanya dama da hijabina ajiki,hijabin da Yaya ta sanyawa suna "hijabin gado"...

Continue reading free chapter

App exclusive

Continue “RAI DAI...” in the app

The author limited this story to mobile. Open the app to read, listen, and keep your place.

Download on the App StoreGet it on Google Play