RASHIN RABOFree

ArewaPen original

RomanceFreeOngoing

RASHIN RABO

  • 1views
  • 59chapters
  • 0audios
  • words
  • 0likes
Start reading

Share:

The story

Synopsis

ongoing

No synopsis yet.

Sample · Chapter 1

RASHIN RABO 1Gun yayi tsit,sai muryar shugabar makarantar ne kawai ke tashi taci gabada fadin wannan hukuncin shine yadace da ku daga yau duk "yar da muka ga batasuturce jikinta ba,kamar yadda musulunci ya umarciduk wata musulma tayi ba,wallahi ni Hauwa sai nawulakanta ta ko yar gidan waye,kuma duk dalibardana ganta da jan baki ko makamancinsa sai nasanya ya shi na goge fuskar da shi,in kuna ja ku aikata ku gani mutanen banza.ta sauke numfashitsahon,sa'a uku taci gaba da fadin."Kuna ganin bayyana surar ga 'ya mace shine zai kawo mata mijin aure shine,zai sa mazansu sankuna da kyau har suyi ra'ayin ku zamo uwarya'yansu,ko da yake wasu lalatattun jahilai sun iyakwasa a haka,ni wallahi a tawa tunanin ina ganinbabu abinda yafi birgewa irin in auri wanda bai san kalar halittata ba,hakan shi zai sa in akayi aurenyafi dokina ya fi tattalina,yanzu zan yi muku misalida yar da ta tsone muku ido,kowa dai yasan cewaYusra tana da kyau duk da suturta jiki da takeyi takare tsiraicinta daga shaidamun mutane kai harma da aljanu haka Kuma duk wani mutumin kwarai zaiso ya rabeta duk namijin daya sam kansa zaiso tazamo matatsa Kai ko Dan iska yafison auren kamammiya irin ta shigarta ta bai hana bayyanar kyaunta ba,muddin kanada kyau koda ka suturce ko ina naka hakan ba zaihana ganin kyawun naki ba."Malamai suka ware masu dangalallun hijabai da masu janbaki Ku koma can masu janyowa mutane masifa a doron kasa,ku dakuke manya kune ya kamata kuyi abinda kananan zasu yi koyi da ku."Agogon da ke daure a tsintsiyar hannunta taduba ta maida kallonta ga daliban,"Yusra Lawan inta shigo makaranta ta fito ta yi mana fadakarwa akanmuhinmancin suturce jiki,ta kuma cika mana daaddu'a a gaggauce."Kana ganinta ka ga shuwa,Yusra 'yar kimaninshekaru goma sha biyar,fara ce sol mai dauke dadoguwar fuska gashin girarta baki suduk masu kauri gashin idonta zara-zara masu kauri,tana dauke dadogon hanci wanda ya dace da doguwar fuskarta,bakinta tamkar an yanka shine da raiza wani abinbirgewa kuma a fuskar tata shine ta yadda kuma ta ke lotsawa yayin da take magana ko tana murmushi,tana da mutukar kyaun jiki dukiyar fulaninta tsayesuke Kam sun dace da tsarin jikinta,duk da rashinwadatar su in ka ganta sai kayi zaton yar wani ministance saboda jikinta a murje yake ga wanisheki da yake yi.Yusra irin matan nan ne,wandaduk tsananin da suke cikin baka isa ka gane ba saidai in kyakkyawan sani kayi mata tana da mutukar hakuri da kunya,ba zaka taba ganinta hada ido daKai ba yayin da kuke magana,komai nata tana yine cikin nutsuwa bata da zaf. cikin takun nutsuwa ta Karaso ta risana har Kasa ta gaida shugabar makarantar hannu tasa ta dagota,ta daga manyanidanunta ma'abacin haske,irin kallon da ake yi matane yasa tayi Kasa da idanun cikin siririyar muryamai dadin saurare,tayi sallama zata fara maganamurya...

Continue reading free chapter

App exclusive

Continue “RASHIN RABO” in the app

The author limited this story to mobile. Open the app to read, listen, and keep your place.

Download on the App StoreGet it on Google Play