FreeArewaPen original
MATAR ABBANA
- 1views
- 30chapters
- 0audios
- words
- 0likes
Share:
The story
Synopsis
No synopsis yet.
Sample · Chapter 1
💘MATAR ABBANA💘 (Luv Story)Writing By Amnah El YaqoubKuyi following Channel dina domin samun zafafan labarai💃🏻👇🏻*** yanda yaso motar tatashi, abun yaci tura, badon yaso ba, haka yajuyo cikin ladabi da girmamawa yadubi Hajiya Kaka yace"Hajiya inaga saide natare muku abun hawa ku qarasa gida,zan kira me gyara yaduba motar,bansan meyasa ta tsaya ba"Hajiya Kaka tasaki ajiyar zuciya sannan ta dubi kyakykywar jikarta, wadda hankalinta kacokam yake kan wayar hannunta qirar IPhone,tace"to hamshaqiya muje, kin hard'e kina danna waya kamar 'yar sarki,mota ta lalace mu sauka munemi abun hawa"Yarinyar da batafi shekara goma Sha takwas ba,daga ganinta kasan surutu bai dameta ba, batace uffan ba, sai baki data ta6e tafara qoqarin bude motar, saide kafin takaiga budewa direban ya zagayo da sauri yabude musu, sannan yazaro wayarsa daga cikin aljihun wandon sa yafara kiran me gyara, yayinda hannunsa na hagu yake d'agashi sama yana qoqarin tare musu Keke napep.Ba'a bar Hajiya Kaka abaya ba, itama hannu tasa tana qoqarin tare musu abun hawan har Allah yakawo wani ya dakata,kafin direban yayi magana Hajiya Kaka tace"tsaya,tsaya,d'an sahu,tsaya ka kwashemu "Dan adede ta ya kalli motar dake gefensu fara tas,qirar Lexus Rs 350 motar sai shining take tana daukar ido,da alama sabuwa ce,nan take yasan cewa yayi babban kamu.Hajiya Kaka tashige, sannan itama jikarta tashiga, direban ya d'an rissina dede wajan da d'an sahu yake zaune sannan yace"G.R.A zaka kaisu"Dan sahu ya kalli Hajiya Kaka yace"Hajiya kudinku dubu uku"Hajiya Kaka tace"muje Allah ya saukemu lafiya"Direban nasu yafara qoqarin dauko kudin zai bayar, Hajiya Kaka tace" 'Dan Ladi barshi zan bashi kudin"'Dan Ladi ya maida kudinsa cikin aljihunsa sannan yace"to Hajiya Kaka saina qaraso,Allah Yakiyaye hanya"Hajiya Kaka tace"A a 'Dan Ladi, zoka kar6i dubu daya kasayi ruwa kasha"'Dan Ladi direba yayi murmushi yace"A a Hajiya Kaka ki barshi"Hajiya Kaka tace"to kanaji ko 'Dan Ladi?,idan angama gyara motar, kana shigowa layin farko kafin kaje gidan Alhaji Biniya,anayin qosai awajan kasiyo min kataho min dashi"Kafin 'Dan Ladi yayi magana d'an sahu yace"Hajiya baku gama bane?"Hajiya Kaka tace"mungama, sarkin azalzala muje,ni Allahn dayayi ni banason kad'ar hankali a rayuwata,ita rayuwa dakake bahaka ake tafiyar da'itaba "Jikarta dake gefe ta dafe kanta da hannunta sannan ta kalli Hajiya Kaka tace" yanzu de tunda yaja mun tafi Kaka kiyi shiru mana,sai mita kike tun dazu haba!"Hajiya Kaka tayi shiru,saide bakin nan nata ta cuno shi gaba alamun fad'an da jikar tata tayi mata baiyi mata dad'i ba.Sun d'auki lokaci suna tafiya wani mutum daga gefen titi yataresu yace"Kabuga"'Dan sahu yace"Drop suka dauka"Sannan yafara qoqarin cigaba da...
App exclusive
Continue “MATAR ABBANA” in the app
The author limited this story to mobile. Open the app to read, listen, and keep your place.