FreeThe story
Synopsis
No synopsis yet.
Sample · Chapter 1
Bismillahir rahmanir rahim.Kowa ya san cewa I'm going to dedicate this book to you Ayunie, the one who always believed in my stories even when they were only scattered thoughts.Yau baka nan, baza ka ga wannan rubutun nawa ba, but I wrote this with your love still holding my hand, and every word carries the part of me that still aches for you. Allah ya jikanka da rahamarsa, Ameen.~ * * ~If there's journey written in my destiny, then why should I stop anywhere, just moving with my own colour without any destination or strings... - AliyuNew GRA, Phase 2, Porthacourt.09:00 AM.Safiya ce, amma idan mutum ya rufe idanunsa ya buɗe, zai ce yanayin na yamma ne bayan rana ta fadi, a lokacin da lumshin duhun dare kewa al'umma sallama kafin baiyanarsa, kuma hakan ya kasance ne sakamakon mamakon ruwan saman da aka kwana aka tashi dashi tun daga daren jiya, wanda duk da a yanzu ruwan ya tsaya sai yayyafi kawai dake sauka hakan bai sa garin ya washe ba.Kuma sai mutane ma suka daɗa bada gudunmawa ta hanyar rashin fitowar su, duk da cewar ranar juma'a ce, ba ƙarshen satin da kowa ke mararin huce gajiyar jikinsa ba, amma duk da haka ɗaiɗaikun mutane ne kawai a waje, da yawa na gida lulluɓe cikin bargo da bacci mai daɗi. Motar ƙirar accord ce, kalar makuba, ta wanku tas cikin yayyafin ruwan sai faman ƙyalli da ɗaukar ido take, tayoyinta a hankali suke motsawa har zuwa wata kwana da allon gefe ya kafe sunan 'Lawson Street' inda kamar koina na cikin unguwar ta sabuwar GRA, layin mai tsananin kyau ne ɗauke da haɗaɗɗun gidaje kala-kala da kuma mikakken titi baki-ƙirin da shima ya wanku cikin ruwan.A cikin motar mutane biyu ne, matuƙin mai suna Jamilu, wanda ba zai wuce shekaru talatin da biyar a ƙiyasce ba sai kuma wata dattijuwar mata dake zaune a baya, Hajiya Laila. Fara ce ƙal! Yafe da wani mayafi kalar ruwan madara da ya ƙara fito da haske da kuma kwarjininta, ga mai kallon da bai san ko wacece ba kenan. Amma ga wanda ya santa, kallo ɗaya ne zai nuna masa irin tsananin fargaba da kuma hanƙoron dake kan fuskarta, don manya-manyan idanun nata basa taɓa iya ɓoye halayen zuciyarta.Hannayen ta duka biyu suna damƙe ne da ƴar jakar hannunta mai cike da tarin takardu da kuma adadin kudi mai yawa, wataƙila kuma ta riƙe jakar ne don kar rawar da jikinta ke yi ta fallasa a idanun Jamilun da tun fitowar su daga hotel ɗin da suka kwana a garin yake bin ta da maganganu na cewar ta kwantar da hankalinta, komai zai tafi kamar yadda suka tsara.Kamar yadda suka tsara.Wani tsari da aka shafe fiye da shekaru tana zana shi a allon cikin ƙwaƙwalwarta, tana hango shi a idanunta sannan kuma tana kawata shi a mafarkin ta... Amma me akace ne? Wai babu wani abu da yake ɗorewa a duniya, a yau duk wannan tsarin da shirye-shiryen ya wuce, yau itace ranar da take ganin zata fuskanci komai. Ta gyara z...
Contents
Table of contents
Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.