FreeArewaPen original
LOKACI...
- 1views
- 47chapters
- 0audios
- words
- 0likes
Share:
The story
Synopsis
No synopsis yet.
About the author
Marubuciya... In za ka fad'i fad'i gaskiya, komai taka ja maka ka biya.
Sample · BABI NA ƊAYA
LOKACI...!"(Mai zuwa da baƙin al'amura)©Fareeda Abdallah1)Da wani irin kasala a jikinsa ya ɗaga idanu a hankali ya sauke kan wayarsa da take ajiye a gefensa.Ƙirjinsa ne ya buga daram! Lokaci ɗaya hankalinsa ya fara ɗugunzuma. Tun kafin ya ɗauki wayar ya ji a jikinsa ba lafiya ba, domin wanda yake kiransa a wayar ba kasafai yake kira ba sai in da wata gagarumar matsalar. "Alhaji? Daman kana ciki? Ƙarar wayarka nake ta ji sai na zaci ko ka zaga banɗaki."Ta ƙarasa maganar haɗe da kai hannunta kan wayar. "Laaa kaga, Khamis ne ma ya ke kira."Amsa kiran da yake gaf da tsinkewa tayi sannan ta kara mishi wayar a kunnensa. "Hello, Hello, Hello Yaya. Kana ji na?"Kalmomin da aka fara faɗa kenan daga can ɓangaren, da wani irin murya mai bayyana mamallakinta yana cikin tashin hankali. "Ina jin ka Khamis"Alhaji Yusuf ya faɗa da sanyin murya, gabansa sai bugawa yake yi. Sai addu'a yake a cikin ransa Allah yasa a wannan karon ba wata mai zafi Khamis ɗin ya sake ɓaro musu ba. "Yaya kana gida ne? Don girman Allah ka taimaka min. Na san a daidai irin wannan lokacin idan kana gari tabbas kana gida, kar ka ce min baka nan don girman Allah Yaya."Khamis ya ƙarasa da salon roƙo, da wani irin rauni da karaya sosai a muryarsa. "Ina gida."Alhaji ya amsa a taƙaice. "Yauwa Yaya, ka ganni a state CID, idan baka zo a wannan lokacin ba wallahi nema suke su tozarta ni su wulaƙantani. Don girman Allah ka taimaka min. Insha Allahu wannan shi ne na ƙarshe..." "Fiye da sau goma sha biyar kana faɗin na ƙarshe Khamis. Me yake faruwa?"Kafin Khamis ɗin ya amsa sai wayar ta katse. Wayarsa ya karɓa a hannunta. A hankali ya ɗaga idanunshi yayi mata wani irin kallo, da saurin gaske ta bar gurin.Zuciyarta cike da zakwaɗin son jin gagarumin rigimar da Khamis ya sake janyowa a wannan karon.Amma ba ta da yadda ta iya, a dole ta fice daga ɗakin. Ta san mijinta da sirri, musamman tsakaninsa da ɗan'uwansa.Ko yanzu da ta ɗaga wayar har suka fara magana a gabanta Allah ne kawai yasa tana da rabon ji.Miƙewa zaune yayi daga kishingiɗen da yake a farko. Yana niyyar danna kiran lambar Khamis sai wani kiran ya sake shigowa. "Ka bari zan kira ka..." "A'a Yaya, ba sai ka kira ba. Ka saurareni don Allah, ina da wadataccen katin da zai isa muyi magana." "Ina jin ka..." "Yaya, wallahi ba wani babban laifi nayi ba. Don Allah don darajar fiyayyen halitta SAW ka zo yanzu. Wacce ta kawo ni gurinnan ba uwa a *** murhu ba iyaye take da a *** murhu.Ƙoƙari take ta toshe min duk wasu hanyoyin da zan iya bi in kuɓuta. Ta rantse da girman Allah sai ta ɗaure ni har igiya tayi rara, ta ce za ta ɓatar da ni a daina jin labarina gaba ɗaya."Ya ƙarasa maganar yana jan wani irin shessheƙar numfashi kamar yana kuka.Hankalin Yayan ne ya ƙara tashi, a zabure ya miƙe tsaye. Ya san Khamis da masifaffen ta...
Contents
Table of contents
Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.