FreeArewaPen original
RANAR NADAMA
- 1views
- 21chapters
- 0audios
- words
- 0likes
Share:
The story
Synopsis
No synopsis yet.
Sample · Page 1
*RANAR NADAMA* (Zombies story) By*©Zahra Royal Star**ROYAL STAR WRITER'S ASSO......**NOTE..... NA SADAUKAR DA WANNAN BOOK ƊIN DAGA FARKONSA ZUWA KARSHENSA GAREKA. (JAMEELU S MUHAMMAD) (Daddy J❤️❤🔥) INA ALFAHARI DASHI A KO INA, ALLAH UBANGIJI YA CI GABA DA KARE KA YA CI GABA DA ƊAUKAKA KA, YA ƊORA KA AKAN MAƘIYANKA, ALLAH UBANGIJI YA KAIKA INDA ZATO BAI TAƁA ZATA BA NA ALKHAIRI......*PAGE 1*University of Tsukuba Japan* Iya ƙarfinta tasa duka tafin hannunta ta hankaɗe ta, tana wani irin ihu ta nunata da yatsa tana faɗin."Idan har ban kawo sanadiyyar rayuwarki ba akan duk wani abu nadasa gaba sai kinzo kin tare min gaba idan har ni naci sunana Ikiram wallahi tallahi saina kawo ƙarshenki Teemah. Har ke wacece a cikin school ɗin nan, ubanki waye shi da har zaki zo kina takara dani akan duk wani buri nawa?, duk wani abu sai kinzo kin toshe min zuwa inda nake son kaiwa a faɗin school ɗin nan, waye ubanki a Nigeria?".Da sauri wani matashin saurayi ya shiga tsakiyarsu, yana duban Teema dake kallon Ikiram dake ci mata mutumci ba abunda take sai kallonta na tsantsar mamakin, suna cikin wannan hali ita tana taƙalar faɗan kwata-kwata yinsa a irin halin bala'in da suke ciki hauka ne da rashin hankali."Ikiram kina da hankali da tunani kuwa?, muna cikin halin mutuwa da rayuwa kina irin wannan furucin?, miye amfanin duk wannan?, ke kina da tabbacin fita a raye daga wannan ƙasar ne iye?, kina da tabbacin wadda zai iya cetonki ne a rayuwa?, ƙika sani ma ko ta sanadiyyar Teemah ɗin da kika raina kika fi kowa tsanarta cece taki rayuwar?, ai baki san ya gobe zaki koma ba, kawai dan ta kasance ta fiki ƙwaƙwalwa ta fiki farin jini a school sai kawai ki ɗauki Karan tsana ki ɗora mata?, duk hakan baisa kin sadudu ba duba da irin cutar data ɓarke mana a school da faɗin ƙasar nan baki ɗaya, ai yasa ku zubar da komai, mu maida hankalinmu wajan ceton rayuwarmu bawai mu tsaya shashanci ba....."Ai wallahi ko wanne irin hali nake ciki ko yafi wannan, bazan taɓa son wannan abar ba, kuma sai inda ƙarfi na ya ƙare wajan rama irin abunda tazo ta tare min, ta rusa mafarkina".Wata irin ƙara ce ta ƙaraɗe gaba ɗaya hall ɗin da suke a tsaitsaiye cike da wani irin bala'in tsoro suka shiga kai dubansu a ƙofar hall ɗin da suka saka kujerun hall ɗin kusan rabinsu suka saka domin kare su daga farmakin zombies ɗin da, da kyar suka suka sami wannan hall ɗin suka fake hall ɗin damƙam yake da jama'a wa'inda suka samu suka shigo hall, baka jin komai sai iface-ifacen jama'a da ihunsu a wajan makarantar da harabar school ɗin.Wata irin zufa Teemah ta shirce tana matsawa kaɗan ta jingina da jikin wani window da ke a cikin hall ɗin, tana jin hawaye na taruwa a cikin idonta wata irin nadama ce ta rufeta lokaci ɗaya, inama ana dawo da baya, da tabbas ko za'a kashe ta baza ta taɓa amincewa...
App exclusive
Continue “RANAR NADAMA” in the app
The author limited this story to mobile. Open the app to read, listen, and keep your place.