FreeThe story
Synopsis
No synopsis yet.
About the author
Nainarh KD – Nkd's “Every heart has a story — I only give it words.” 📞 Phone Number: *** or ***
Sample · 1
SON ƘAUNA...🔥🏃💔_An ƙaddara su su ƙaunaci juna, an ɗaure su da nauyin iyali, zuciyarsu ta fashe sakamakon ƙaddara.NOTE*Na sadaukar da wannan littafi Mai Taken SON ƘAUNA ga dukkan yaran da aka yasar a faɗin duniya: ma'ana sadaukarwa ce ga duk wani yaro da ya tsinci kansa a Rayuwa ba tare da wani nasa ba.*Story & Written By_Nainarh KD⁂𝒩𝓀𝒹𝓈❦♡_Copy is not allowed.¡!Ba kuma zan Lamunci a canzan labari kota wata siga ba.¡!MARUBUCIYAR:1. Sarauniyar Kyau 2. Tsantsar SO 3. Aneeserh (Innocent Girl)4. Kin cuceni5. Ranar biyan buƙata (rai ba'a bakin komai yake ba)6. Ba Tabbas 7. Captain Ayusherh 8. Ummul-Jaannah9. Ba Riba 10. So Dan Rayuwa And Now SON ƘAUNA!01Kaɗan daga cikin tarin tambayoyin dake kara-kaina cikin kwakwalwar kanta shi ne wace ce ita? Sannan cikin waye a tare da ita? Waye uban cikin? Shin ta wani hanya aka samar da cikin?E tabbas tana da buƙatar sanin hakan domin ta hanyar sanin hakan ne zata sama amsar duk wasu tambayoyi dake jibge a kwanyarta.Son tasan wacece ita da takeyi ba wai don batasan kanta bane ko kuma ta manta wacece ita a'a sam duk da dai kusan hakan ne amma da banbanci.Wani ɗan ɓangare kaɗan na cikin Rayuwarta takeson sani ɓangaren da ya zama mafari na sabuwar ƙaddararta ɓangaren da ta kasa tuna komai a kai tun bayan farkawarta ta tsinci kanta a gadon asibiti ɗauke da ciki na tsawon watanni tara.Tabbas ta shiga ruɗani, tashin hankali da kuma firgici domin duk iya kar ƙoƙarin ta a kan ta san gaskiyar abin da ya faru da ita shekara guda baya tun bayan barowarta daga garinsu amma abu ya cutura.Ta yi kuka ta yi kuka sannan ta addabe kanta a kan ko ya ya ne ta samu ta tuna abin da ya faru har ta tsinci kanta da ciki haihuwa Yau ko gobe bayan tasan ita dai budurwa ce amma garin ya ya ta rasa wani ɓangare na tunanin ta sannan duk iyakar binciken Likitoci basu iya gano ko wacce matsala ba ko dalilin da ya sa ta sama shafewar tunani.Gaba ɗaya duniyarta ta juya zuwa wata kalar duniya mai cike da tashin hankali tun da ta baro asibiti sannan ta shiga mota domin zuwa garinsu duk da batasan da wani baki ko wasu kalamai zatayi ma mutanen ƙauyensu bayani ba ta sani Mahaifiyarta zata iya fahimtarta to amma mahaifinta da ya kasance shugaban ƙauye fa ga kuma yayanta mai jan ragamar ƙungiyar nan ta fusatattun matasan ƙauyen nasu masu ɗaukar hukunci a hannu a kan duk wani abu da ɗan ƙauyen nasu zai aikata wanda ya saɓa wa addini da al'adarsu.Ita kam bata da wani wurin zuwa in ba ƙauyen nasu ba sai dai tana fargaban abin da zata tarar acan ɗin.“Ke Mata! Ke Matar nan ki tashi mana an iso inda zaki sauka!”Maganar da taji a dodon kunnenta cikin tsawa-tsawa shi ne ya sa ta buɗe idanunta da suke lumshe sai dai sun yi wani irin ja, ...
Contents
Table of contents
Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.