CI MA ZAUNEFree

ArewaPen original

ActionFreeOngoing

CI MA ZAUNE

  • 1views
  • 32chapters
  • 0audios
  • words
  • 0likes
Start reading

Share:

The story

Synopsis

ongoing

No synopsis yet.

Sample · Chapter 2

CI MA ZAUNE*                     NA       MAMAN AFRAH                  🅿️2️⃣    "Ki wanke mini farar shaddar nan ki goge mini" Ya ce yana haɗe rai zai juya ya koma waje, da to Aminar ta amsa duk abin da ake Dada tana kallon su ta gefen labule."Sabo! Sabo!! Sabo!!!" Dada ta shiga ƙwala masa kiran  sunansa muraran yau babu Alhajin ma, ganin ya shigo gidan tamkar bai san tana nan ba, bare ya je ya gaishe ta. Sai da ya ɗan yi jim sai kuma ya amsa a shelaƙe."Iyee" Ya ce a daƙile maimakon ma ya ce na'am ran Dada har zafi yake ba don tsoron habaicin kishiyoyi ba da a yanzu zai sakar mata ƴarta. A bakin ƙofa ya tsaya bayan ya buɗe labulen ua tsaya getsetse a kan Dada da take zaune a kan kujera yana riƙe da ƙugu. Wani takaici ne ya dirar mata tana jin tamkar ta hau cikin nasa da duka ko ta rage damuwa."Ya aka yi ne" "Au Allah gaskiya ne Sabo ni za ka nunawa salalan tsiya? Ni za ka sincewa zani a kasuwa na ɗauki ƴar budurwa gagal a leda na baka amma ko wata ba a rufa ba gaisuwa ma ban isa ka gaishe ni ba?""Yo ai mun gama bajat ni da ke kuɗi dai kika aura mata kuma na sha baku shi kafin na aure ta kun gama cin rabonku yanzu kuma sai yadda hali ya yi sai abin da kuka gani" Ya ce yana saka hannu a aljihu ya ɗauki naira ashirin ya ajiyewa Dada a kusa da ita wai ta sayi goro ya juya ya fita Amina tana jin daɗi da bai ga miyar da Dada ta zubar ba bare ya mata faɗa. Lallaɓowa Amina ta yi ta zauna ta doka uban tagumi."Oh ni Saude in da ranka ka sha kallo, ashe mutumin nan lumbu-lumbu ne wutar ƙaiƙayi ita bata ci ba ta haɗe ko ina da hayaƙi, yanzu lalacewar son kuɗin nawa har ya kai a ɗauki murtala (20) A ce na sayi goro wato ga wacce talauci ya gama baibayewa, ni Saude ina zan kai wannan bala'in wannan abin kunya da mai ya yi kama har nake kasa fitowa daga ɗaki, ni ban san ba ma ko dai su Ladiyo suna da labarin halin da kike ciki nake musu kallon biri suna mini kallon ayaba" Ta ce tana doka wani uban tagumi ga yunwa tana ƙwaƙular ƴaƴan hanjinta."Ki yi haƙuri Dada wannan ce ƙaddara ta""Ah ah zan yi duk yadda zan yi ko mai gari sai na kai masa ƙara ya raba wannan auren" Da wannan ta baro gidan riƙe da ledar vivan da ta saka zanin Amina da ko wanki bashi da shi don ta yi basaja kar a ce bata kawo komai ba, a yi gulmarta ko a yaɓa mata magana kasancewar zama da kishiyoyi komai kake yi a ido yake.   A inda ta wuce su Sabo yanzu ma suna zaune ko kallo basu ishe ta ba yunwar cikinta ma ta ishe ta, lokacin ana sallar la'asar ta shiga gida ita da ta ce sai dare sai ga shi rana ma ko sanyi bata yi ba ta dawo bare a yi zancen dare. Rai ta haɗe ta shigo tana muzurai."Ga Dada ga Dada yau akwai wankin baki auren mai kuɗi akwai r...

Continue reading free chapter

App exclusive

Continue “CI MA ZAUNE” in the app

The author limited this story to mobile. Open the app to read, listen, and keep your place.

Download on the App StoreGet it on Google Play