FreeArewaPen original
DAFI
- 1views
- 60chapters
- 0audios
- words
- 0likes
Share:
The story
Synopsis
No synopsis yet.
Sample · SHAFI NA BIYU
DAFI💥ByMAMAN BOYSHAFI NA BIYU >>>>>>>>>>>>>>>ASIBITIN ƘASHI NA JANAR AHMADI RIMI ,B'ATA GARAWA LOCAL GOVT ,KATSINA8:16am.A yanayin da motar ujila haɗe da motar gidan yari suka danno kai a cikin farfajiyar asibitin yadauki hankalin mutanen da ke harkokinsu a wurin . Duk da safiya ce sannan yanayin gari na ruwa da ruwa kancigaba da sauka ahankali da rangwamen iska da sauti, hakan bai hana wasu tsayawa ganin nau in majinyacin da aka shigo dashi ba .wanda masu kallo awurin basa bukatar karinbayanin cewa koma waye majinyacin daga gidan gyaran hali aka dauko sa . .Tunkafin fito da majinyacin tuni nurses sun fito da gadon dora mara lafiya batare da bata lokaci ba aka fito da marar lafiyar bursunar aka nufi dakin bada agajin gaggawa domin ceto rayuwar sa.Duk nacin mai kallo da ƙwaƙwaf alokacin bai isa ya iya tan tance jinsin wanda ke shimfide a gadon ba sakamakon wata iska mai karfi da ta huro ta kaɗa ruwan dake sauka da karfi alokacin. Gab da nurses zasu shiga dakin ne daya daga cikin su ta juyo a hanzarce tana duban daya daga cikin ma aikatan gidan gyaran halin da cewar "ku jiramu anan."Bata bi takansu ba ta rufawa kwararrun likotocin da suka ratsa ta gefenta suka shige cikin dakin baya ...Dolen su suka tsaya anan bakin kofa a reception ,Daya daga cikin Gandre bobin da ya kasance babbansu kuma namiji ya dubi abokan aikinnasa biyu da suka kasance mata ,ya furzar da iska kawai cikin wani irin yanayi .Ahankali ya soma kai da kawowa acikin reception din tare da tsumayin jiran jin ta bakin likitocin su kuwa matan basu motsa daga bakin kofar da suke ba sun kasa sun tsare sai faman muzurai suke yitsurarun jamaar da ke cikin reception din kuwa sai kallonsu suke .Ta cikin ruwan saman da ke sauka alokacin idanunsa suka sauka awajenn reception din akan motar yansandan da ta shigo asibitin . ,bata nufi wurin da aka tana da dan ajiye motoci ba ta yi parking dai dai kofar reception ..Saida gaban gandiroban ya yanke ya fadi ganin yan sanda biyu cikin uniform da dayan kuma jami in sirri ne da yayi shigarsa cikin kananun kaya sai katuwar bakar coat a jikinsa,dasauri suka tara lema ga inspector din dasu kansu dan sukare kansu daga ruwan sama .Gandirovern kuwa yayi saurin fitowa daga reception yanufo su ta inda ruwan bazai jika shi ba ya tsaya a balcony ..Su na karasowa suka yimasa sallama tare da mikamasa hannu suka gaisa ,ba sai an sanar dasu ba shine suke son ganin shigarsa ta cikin uniform din aikinsa ya nuna masu shi din waye .."Sunana inspector yahaya haladu ,daga hukumar yansanda ta farin kaya atare da ni akwai abokan aikina ..Yafada yana cirowa gandirobar ID card dinsa na shaidar aikinsa kafin ya cigaba da cewa "game da case dinnan na abinda ya faru a gidan yari adaren jiya munsamu rohoto ne a...
App exclusive
Continue “DAFI” in the app
The author limited this story to mobile. Open the app to read, listen, and keep your place.