MAWAHIBFree

ArewaPen original

RomanceFreeCompleted

MAWAHIB

  • 1views
  • 30chapters
  • 0audios
  • words
  • 0likes
Start reading

Share:

The story

Synopsis

completed

No synopsis yet.

Sample · 1

💗MAWAHIB💗 (Hot luv) Writing By Amnah El Yaqoub1&2Mawahib littafin kudi ne, kibiya 500 kacal ki karanta cikin salama 0164549488 Amina muhammad GTbank Kokuma katin MTN ta wannan number *** _____'Yanmata ne guda biyu suke tafiya cikin nutsuwa,kana ganinsu kasan bazasu wuce shekaru goma sha takwas ba,d'ayar tana Sanye cikin uniform na islamiya,tanada duhun fata kad'an,a hankali ta juya ta Kalli qawar tata, wadda take Sanye cikin kayan gida,babu uniform din ajikinta saide dogon hijab irinna d'ayar,wanda yazo mata har qasa,kalar hijabin ruwan toka yayi mutuqar qawata farar fatarta,Wanda kana gani kasan cewa hutu dakuma Jin dadi ya ratsa fatar tata. Jiddah tace"MAWAHIB,kiraba mana musu dan Allah"Ahankali tajuyo dara daran idanunta wanda yayi kama Dana mejin bacci, ta Kalli qawar tata, sannan tace"musun me Jiddah?"Wadda aka Kira da Jiddah tace"wallahi musu muke dasu Hassan da Hussainin gidanmu,nace duk unguwar Nan sukadai ne 'Yanbiyu matasa, shine sukace min wai Yaya ASHRAF din gidanku Shima 'Yanbiyu,nikuma nace ba 'Yanbiyu bane, Yaya Ashraf ne kadai yayanku,saboda nide tunda nake dake,Kuma duk yanda nake qawance dake,baki taba cemin kunada 'yanbiyu a gidanku ba"Saida ta yatsina kyakykywar fuskarta mai cikeda gashin gira alamun batason maganar, sannan ta motsa dan qaramin bakinta Mai launin pink,tace" 'yanbiyu ne,d'ayan baya zuwa sosai shiyasa baki sanshi ba,ai kinsan Yaya Ashraf dinko?,toshima d'ayan kamar kinsan shi,yanda kikaga Yaya Ashraf Shima haka yake,yana Nan kullum yana fama da uniform,basuda banbancin kamanni, komai nasu iri dayane,nikaina idan suka hadu su biyun bana Iya banbance su,saboda komai iri daya suke sakawa,kawai de hali ne kowa da irin nasa"Cikin mamaki Jiddah tace"ashe Ana Samun 'yanbiyu maza manya kamar Yaya Ashraf,? Amma Mawahib baki taba bani labarinsa ba"Cikin sauri Mawahib tace"menene hadina dashi dazan baki labarinsa? wannan marar imanin inani inashi?, halinsa daya da mahaifiyarsu,duk yanda kike tunaninsa yawuce Nan,miskilancinsa yayi yawa,baida fara'ah,kenifa bari Kiji Infada miki na tsaneshi, tun saudaya dana ta6a yimasa laifi ya Sumar dani, daga ranar naji nasake tsanarsa"Cikin sauri Jiddah ta zaro ido(😳)Tace"nashiga uku Suma fa kikace?"Cikin tabbatar wa Mawahib tace"suma kuwa,Ina zaune Yaya Ashraf yazo yacemin naje nagyara masa dakin su,Wai ashe shine zaizo daga Abuja,nikuma bansan ranar zai dawo ba,dana gama gyaran saina dan kishingida akan gadon su,nadan dora kaina a wani fillo Mai laushi,Bansan lokacin da bacci ya daukeni ba,daya dawo yaganni a'inda yake kwanciya,kuma nadora kaina akan fillonsa, shine ransa ya6aci,daya damqi gashin kaina bansan lokacin dana saki ihu ba,shine yasaka kaina a cikin sink din toilet dinsu yabude ruwan,nide nasan yasakani a ruwa,amma daga Nan bansake sanin inda kaina yakeba,Sai f...

Continue reading free chapter

App exclusive

Continue “MAWAHIB” in the app

The author limited this story to mobile. Open the app to read, listen, and keep your place.

Download on the App StoreGet it on Google Play